Duk wanda ya san abunda ake kira Shugabanci da irin nauyin da ya rataya a wuyan shuwagabanni, ya kuma kalli halin ko-in-kula da Gwamnatin jahar Zamfara ta yi da halin ni-'ya-sun da al'ummar jahar Zamfara mu ke ciki. Musamman mutanen karkara.
Kamar yadda mu ka sani babba daga cikin ginshikan abubuwan da su ka rataya a wuyan shugaba su ne kariyar rayukka da dukiyoyin al'umma.
Wanda Idan muka dubi yadda ake kashe al'ummar jahar Zamfara, ana kone dukiyoyinsu, ana garkuwa da mutane, fyade ga mata da kuma kisan kiyashi. Misali yau kurrum da ke wannan rubutun kusan dukkanin kauyukkan da ke garin Gusau Gundumar Mada sun tarwatse, Inda aka kashe mutun goma sha hudu a cikin kauye daya aka kone duk wasu Hatsi da al'ummar yankin suka noma, a wannan shekarar. Bayan kashe yayar Sanata Mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya da 'yan ta'addar su ka yi ta hanyar harbinta a baki kamar yadda kafar yada labarai ta BBC HAUSA ta bayyana yau 5-2-2019 cewa yan ta'addar sun yi garkuwa da mijinta da wata mata da itama ta rasu.
Haka zalika yau din nan da na ke magana an yiwa al'ummar wani kauye da ke Gundumar Gungurmi a karamar hukumar Bungudu kisan mummuke Wanda har jami'an tsaron da su ka zo kawo dauki abun ya fi karfinsu. Wanda Hakan ne ya sa barayin su ka yi yadda su ka so.
Jiya-jiya mun yi hira da wasu 'yan gudun Hijira da suka fito a wani kauye mai sunana Kukoki a karamar hukumar Zurmi, Wanda sun tabbatar da duk wani kauye da ke zagaye da su yanzu ya zama kufai. Su Kansu garin nasu mai gida sama daruruwa yanzu babu mutun hansin cikinsa, duk sun tsere.
Hanyar Magami zuwa Dangulbi zuwa Dankurmi Tuni ya buwayi 'yan Kasuwa da al'ummar yankin, domin kullum sai an kashe mutane ba gaira ba Dalila. Hakan ya sa dole yan Kasuwa sun Dena zuwa mazauna garin dole a bi ta Anka in ana bukatar shigowa garin Gusau.
Haka abun ya ke Idan ka duba kusan kowane lungu da sako na jahar Zamfara cikin tashin hankali mu ke.
Sai dai kash! Duk wannan kisan mummuke da ake yi Muna da nufin sai an karar da mu daga doron kasa, bai sa Gwamnanmu ya yi ko gezau ba. Hasalima Muna ganin yafi darajjanta sha'anin siyasarsa da rayuwa da dukiyar al'ummar jahar Zamfara. Hujja a nan ita ce; duk wadannan kashe-kashen da kullum ake yiwa Zamfarawa, tun hawan mulkin wannan Dan tahaliki, ba a taba ruwaito Inda hankalinsa ya dugunzuma har ya mayar da hankalinsa duka ga sha'anin tsaron ba.
Hasalima mu talakawan jahar Muna ganin kwata-kwata ba kisan da ake yi Muna ne gabansa ba. Domin ko jajen da ya taba yi gare mu akan kisan kiyashi da ke yi Muna bai wuce uku ba. Daya na yar Galadima, sai na biyu a Anka da daya na kuma karshe da ya yi a Masarautar Zurmi, Wanda ko shi din ma Muna ganin Gwamnonin katsina da Sokoto su ka cilasta masa Bayan sun kammala mitin da shugaba Buhari a Daura, wanda yana kammala wannan jajen ya taka jirgi ya yi gaba zuwa Jamus a lokacin.
Babban abunda ya ke ba mu mamaki shi ne, lokacin da 'yan Majalisar jaha suka yi yunkurin tsige shi. Da lokacin da uwar jam'iyar APC ta Hana shi yiwa talakan Zamfara doki dora. Ba Wanda bai ji da ganin bacin ransa ba a duniyar nan.
Amma abun mamaki, duk da cewa jam'iyar APC har yanzu ba ta da 'yan takara jahar Zamfara. Wannan Tahaliki zai iya kwasar al'ummar jahar yana yawace-yawace da sunan tallata Dan takarar da ya ke fatan ya gaje shi, duk da har yanzu ba su San makomarsu ba. Maganar tausayawa ko zuwa jaje ko ma daukar matakin da ya dace domin kariyar rayukkkan wadanda ake farautar rayukkansu, ba ta ma taso ba.
Wanda Hakan ya tabbatar Muna da cewa sha'anin siyasa ya fi rayuwar al'ummar jahar Zamfara tasiri ga Gwamnan jahar domin zai iya bata lokacinsa de kudin talakawa gare su, Amma baya iya Kula da halin ni-'ya-sun da al'ummar jahar ke ciki.
Da haka mu ke Kira sa babbar Muryar ga mai girma Gwamna da ya aje Maganar yiwa wani yakin neman Zabe gefe daya, ya Kalli halin da mu al'ummar jahar mu ke ciki. Ta hanyar shawo kan matsalar tsaron da ke daukar rayukkanmu da dukiyoyinmu a kullum.
Allah ya sa Kokenmu ya Kai ga kunnuwan wadanda mu ka yi shi domin su, ya kuma ba su ikon share Muna hawayenmu, Allah muna rokonka ka amintar da mu da zaman lafiya Mai Dorewa a jahar Zamfara da kasarmu Nijeriya baki daya. Allahumma amin.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
5-2-2019








