YAN ACABA HAR YANZU BA SU BAR MURNAR FADUWAR YARI, A GUSAU BA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 25 May 2019

YAN ACABA HAR YANZU BA SU BAR MURNAR FADUWAR YARI, A GUSAU BA!



Tun Bayan da Kotun kolin Najeriya ta bayyana cewa jam'iyar APC ba ta yi zaben fitar gwani a jahar Zamfara ba, kuma zaben da aka yi mata ya zama na banza. Wanda Hakan ya nuna cewa wanin su ne za a baiwa jahar Zamfara.


'yan Acaba su ka cika garin Gusau, suna ta murna akan wannan hukucin. Wanda duk Inda ka tarar dan Acaba za a ji yana fadin;  "Alhamdulillahi, Allah ya fitar damu daga kangin da mu ke ciki " na yi kokarin zantawa da wasu daga cikin 'yan Acaba din da su ka bayyana Mani cewa; "mu matsalar mu daya, ita ce zaluncin da Shehi ya yi Muna na Hana mu sana'armu a Shekaru hudu baya yanzu ya zo karshe".


Sharhi:


Hakika yan Acaba sun shiga halin kaka-ni-kayi a jahar Zamfara. Saboda dokar zalunci da aka dora masu ta takaita yawo da babura daga wani lokaci zuwa wani lokaci. Dokar da ba wai yan Acaba kurrum ta taba ba ta taba zamfara ne baki daya.


Dan haka Muna fatan Sabon kwamna ranar da ka hau mulki Abu na farko da za ka Fara karyawa da shi, shi ne cire wannan dokar zaluncin domin sanyaya rayuwar al'ummarka.


Allah ya ba Sabon gwammnan zamfara ikon kwatanta gaskiya da adalci a Yayin Jagorancinsa.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau


20-9-1440

25-5-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here