BABBAN LABARI. MAGOYA BAYAN SHEHI SUN RABA GARI DA SHUGABA BUHARI. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 25 May 2019

BABBAN LABARI. MAGOYA BAYAN SHEHI SUN RABA GARI DA SHUGABA BUHARI.




Magoya bayan Gwamnatin jahar Zamfara, Sun yage hoton shugaba da ke bakin Goverment House Gusau. Wannan ya biyo Bayan hukuncin da kotun kolin najeriya ( *Supreme Court* ) Wanda ya haramta damar APC na tsayawa takara baki daya. Kuma Wanda ya baiwa yan takarar jam'iyar PDP (galibi) damar zama zabbun Shugabannin Zamfara.


Yayyage hotunan dai na nuna rashin jin dadin su ga yadda Shugaban ya ki mara masu baya, domin samun nasara a Shari'ar da aka yi suka sha Kaye.


Yanzu dai Kallo ya koma sama, shin za su bar jam'iyar APC ne ko za su hakura su zauna, Amma ba su tare da shugaba Buhari.


Masu hasashe dai na ganin da wahala magoya bayan Shehi su zauna a APC saboda yanayin da su ka samu Kansu.


Ko dai mene ne lokaci zai nuna.


Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here