ANA BARIN HALAT DAN KUNYA.... WASIKA ZUWA GA SANATA HASSAN NASIHA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 22 June 2019

ANA BARIN HALAT DAN KUNYA.... WASIKA ZUWA GA SANATA HASSAN NASIHA.


Tun a farkon makon nan da labari ya fita cewa sanata Mai wakiltar Zamfara ta Tsakkiya ya nada 'ya'yansa Guda biyu daya a matsayin PA daya kuma a matsayin SLA. Labari ya cika wannan kafar kowa yana fadin albakacin bakinsa. Masu kushe na matakin gaba, masu ganin matakin na kan hanya ya ke na biye masu baya.

Hakika in za mu dubi maganar gaskiya, sanata Hassan Muhammad Nasiha , yana da damar ya zabi wadanda ya ga dama ya nada su a matsayin masu taimaka masa. Waya Allah Dan matukar son Da ya KE yi masu ko Dan cancantarsu, ko wahalar da su ka yi da shi. Wanda Da wannan damar ne sanatan ya yi amfani wajen nada 'ya'yansa. Domin su taimaka masa a majalissar dattawa ta kasa, Da zai wakilci yankin Zamfara ta Tsakkiya har zuwa 2023 in muna raye.

Sai dai maganar gaskiya Da yawa Dan Adam yakan kyale abunda ya halatta gare shi domin kunyar idon wani ko wasu.

Idan Mu ka dubi siyasa da yanayin yadda ake gudanar da ita. Duk Dan siyasar Da ke bukatar nasara, zai rinka kula da duk wani Abu Da zai iya kawo masa farin jini ko akasinsa.  Wanda hakan ne, ke sa 'yan siyasa kan yi kokarin kaucewa raba mukamai a bangare daya na al'ummar Da su ke jagoranta. Domin tabbatar da Kowane bangare na al'ummar an jawo shi an tafi tare. Hakan ne ma ya sa da wahala ka ga Dan siyasa ya dauki mukamin siyasa ya baiwa Dansa, yarsa ko matarsa ko Da kuwa sun cancanta. Hakan na tabbatar da bai rasa nasaba Da tsoron bakunan mutane na allah waddai, kamar yadda aka yi ta yi maka.

Mai girma sanata, hakika yanzu muna a wani lokaci na siyasa Da aka wayi gari abubuwa su ka yi tsauri, a siyasance. Musamman a jahar Zamfara, Domin na tabbatar Zaben 2023 za a yi zaben kai-da-halinka ne. Dan haka, ina ganin da za ka Kalli shawararmu da za ka debe wadannan 'ya'ya naka tare da Maye gurbinsu da wasu Da su ka wahala da Kai. Domin ko ba komi duk abunda ka samu wadannan 'ya'ya naka ka samawa wa. To MI zai hana ka dauko wasu na waje Dan su amfana, har su ma gidajensu su tsayu kamar yadda naka ya tsayu.

Allah ya sa wannan takaitacciyar wasika tawa ta riskeka ka, ka kuma yi amfani Da ita, Domin gyaran siyasarka

Muna rokon Allah ya Baku ikon yi muna jagorancin kirki da wadanda su ka gabace ku ba su yi muna ba.

 Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

22-6-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here