Tsohon gwamnan jahar Abdulaziz Yari Abubakar ya bar bashin bashin N251, 951,849,482.50 ga sabuwar Gwamnatin, Gwamna Mohammed Bello Matawallen-Maradun.
Wannan jawabi ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin karbar mulki, Mallam Ibrahim Wakkala Muhammad. Lokacin da kwamitinsa ya ke ganawa da manema Labarai a fadar Gwamnatin jahar Zamfara Da ke Gusau.
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa gwamnati Mai Ci a yanzu ta kafa wannan kwamitin ne. Domin gano iya adadin basukka Da gwamnatin Da ta shude ta Bari, Kafin Mika ragamar mulki ga wannan Gwamnatin.
Wannan rahoton na biyar rahoton Da tsohowar Gwamnatin Da ta gabace mu ta yi ne. Wato kwamitin Mika mulki. Kurrum.
BASHI DA AKA BARI NA AYUKKAN DA BA A KAMMALA BA:
Jimillar bashin da da aka Mika muna na tsohowar Gwamnati na ayukkan da ba a Kammala ba. A bangaren tattalin arziki, Muhali da kuma sha'anin gudanarwa da kuma na bangaren Zaman jama'a sun Kama naira N151, 190,477,572.02 (Biliyan dari Da Hamsin Da daya, da Da miliyan dari da tis'in da dari hudu Da saba'in da bakwai da dari biyar da saba'in da biyu Da kwabo biyu).
BASHI NA MA'AIKATAR KUDI:
Wannan ya hada Da basukkan da ba a biya ba, kudin Jiran ingancin aiki ya Kammala. Kudin Bailouts Da kuma bashin banki kudin sun Kama naira N65, 361,873,755.75 ( Biliyan sittin da biyar da, miliyan dari uku da sittin da daya Da dubu dari takwas da saba'in da uku, da dari bakwai da Hamsin da biyar da kwabo saba'in Da biyar).
BASUKKA DA AKA BARI A MA'AIKATAR KANANAN HUKUMOMI DA LAMURAN MASARAUTU:
A wannan ma'aikatar Nan ce ta zama ma'aikata aka fi zukar kudin Al'umma. Domin akwai adadin naira N35, 399,498,154.53 ( miliyan talatin Da biyar, Da miliyan dari uku da Da tis'in da tara Da dyau dari hudu da tis'in da takwas Da dari daya Da Hamsin Da hudu da kwabo Hamsin da uku) da aka rubuta ba tare da an fadi abunda aka yi da kudin ba.
A debe wasu kudi na National Housing Fund (NHF) Domin tallafawa ma'aikata su mallaki gidaje Kafin su ajiye aiki tare da kudin fanso Da ake debewa ma'aikata Domin mora in sun ajiye aiki wadanda su ka Kama naira N1, 431,645,305.99 ( Miliyan daya Da miliyan dari dari hudu Da talatin Da daya Da dubu dari shida Da dari uku da biyar da tis'in da Tara) Da aka debe a albashin Ma'aikata. Daga Shekara ta 2016 zuwa 2019 dukkan wadannan kudaden ba a sanya su a hukumomin ba.
BASUKKAN DA AKA SAMU A MA'AIKATAR ILIMI:
Bangaren ilimi yana daga cikin hanyoyin bunkasar cigaban Al'umma musamman ta fuskar ilimi domin Samar da Al'umma Mai nagarta, tare kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara, a bangaren akwai kudaden har kimanin Naira N2, 812,172,155 ( biliyan biyu da Miliyan dari takwas da goma sha biyu, da dubu dari da saba'in da biyu Da dari da Hamsin Da biyar) da ba a yi bayanin yadda aka yi Da su ba. Amma an bar yayan talakawan zaune ba tare da cigaba Da karatu ba, Saboda rashin Biyan kudin Waec Da Neco kamar yadda Gwamnatin ta alkawarta za ta yi.
Gwamnatin da ta shude ta yi ikirarin ta biya kudaden garatuti na ma'aikatan gwamnatin da su ka bar aiki, tare da fitar Da kudinsu kimanin naira N2, 000,000,000 (Biliyan biyu) Wanda kwamitin tsohon gwamnan ya gano tsofaffin Manyan sakatarori kurrum ne, aka biya hakkokansu. Wanda Hakkin nasu shi ne N400, 000,000 (Miliyan dari hudu) Kurrum. Sauran naira N1. 6 billion (Biliyan daya da miliyan dari shida) Ba a san inda su ke ba.
Wadannan Kadan kenan daga cikin abubuwan da kwamitin karbar mulki Wanda gwamnan jahar Zamfara, Alhaji (Dr.) Bello Mohammed Matawallen-Maradun Ya nada tsohon mataimakin gwamnan jahar Zamfara, Mallam Ibrahim Muhammad Wakkala. Ya jagoranta
YUSUF IDRIS G
Babban Daraktan Watsa Labarai Na Gidan Gwamnatin Jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
24/06/2019

