LABOUR ROOM GLOBAL INITIATIVE, ZA TA CIGABA DA AIKI TUKURU, DOMIN CIGABAN ZAMFARA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 28 June 2019

LABOUR ROOM GLOBAL INITIATIVE, ZA TA CIGABA DA AIKI TUKURU, DOMIN CIGABAN ZAMFARA!


A shekara ta 2017 wannan kungiya ta shirya shiri irinsa na farko da ya Tattauna matsalolin Najeriya inda Kowace jaha, matashi daya ya wakilce ta. Alhamdulillahi jahar mu na daya daga cikin jahohin da ba a bar mu a baya ba. Wanda Ambassador Nura Isah Gusau ya wakilci jahar Zamfara. Wanda alhamdulillahi jahar Zamfara na daga cikin jahohin Da wadanda na wakilce ta ba su yi kwanan kawai ba...

Alhamdulillahi bayan an Kammala wannan Shiri mu jagororin wannan tafiyar a jahar Zamfara, mun ga bai dace, yadda aka Tara jajirtattun matasa maza Da mata, a kungiyar a watse bayan Kammala shirin Labour Room Reality TV SHOW ba. Dan haka mu ka ga ya dace mu dunkule mu kafa, kungiya Mai manufar agazawa al'ummar jahar Zamfara musamman matasa Da mata ta fuskoki da dama. Dan haka mu ka yi kokarin yiwa kungiyar register da hukumar Da ke yiwa kamfanoni da kungiyoyi register (CAC). Wanda alhamdulillahi bayan kammalawa mun dukufa wajen ganin mun daidaita jagorancin kungiyar a matakin jahar Zamfara baki daya.

Biyu daga cikin shiraruwan da mu ka yi a shekarar da ta shude su ne;

1- Mun gudanar da shirin #Keep_Zamfara_Clean shirin da mu ka gudanar da zummar zaburar da al'ummar jahar Zamfara da su rungumi dabi'ar tsabtace muhali. Wanda mu da kanmu mu ka shiga cikin garin Gusau muna tsabtace muhali tare da kwashe Shara a guraren da duk bai cancance ta ba. Tare da raba Mukalu masu dauke da jan hankali akan illar zubar Da Shara barkatai da muhimminci tsabtace muhali.

2- Ganin siyasa ta kunno Kai ana ta fadace-fadace har an Fara daukar rai. Mun yi wani shiri Da ake Kira. #Movement_for_political_Sanity_in_zamfara Wanda mu ka yi yin gangami da ya samu wakilci a dukkanin kananan hukumomi 14 da ke jahar Zamfara. Inda Mu ka yi ta Kira ga 'yan siyasa a Kowane lungu da sako na jahar Zamfara  da a yi siyasa ba da gaba-ba.

Da sauran ayukka matara Kama da haka.

Wanda zuwa yanzu mun yi kokarin tsara tsarin jagorancin kungiyar kamar yadda ya dace. Kuma muna maraba da duk wani Wanda zai zo da shawara ko neman a dama Da shi Domin cigaban jahar Zamfara. Ba tare da kallo jam'iya ko fahintarsa a rayuwa ba.

Dan haka insha Allahu, yanzu za mu cigaba Da aiki tukuru. Ganin mun bayar da gudunmawarmu Domin cigaban jahar baki daya.

Muna rokon Allah ya rika muna, ya ba mu ikon aiki tukuru wajen tallafawa rayuwar Matasa da ma jahar Zamfara, baki daya.

 *Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau, SA Media And Publicity























Post Bottom Ad

Responsive Ads Here