GWAMNAN JAHAR ZAMFARA YA GANA DA TSOHON SHUGABAN KASA, JANAR YAKUBU GAWON - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 29 June 2019

GWAMNAN JAHAR ZAMFARA YA GANA DA TSOHON SHUGABAN KASA, JANAR YAKUBU GAWON






Gwamnan Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya gana da tsohon shugaban kasa na mulkin Soji, janar (Murabus) Yakubu Gawon, a fadar Gwamnatin jahar Zamfara Da ke Gusau.


A lokacin da ya ke jawabi tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa, shi Da tawagarsa sun shigo jahar Zamfara, a cigaba Da rangadin Da su ke yi, Da sauran takwarorinsa, Domin neman nadin kan al'ummar Najeriya Domin kawo karshen yaduwar tashe-tashen hankulla ta amfani da bambancin addini da kabilanci, da ya zama ruwan dare game duniya.

Haka zalika tsohon shugaban kasan ya taya, gwamnan murnar zama gwamnan jahar Zamfara, ya kuma roki Allah ya ba shi ikon sauke nauyin Da a aka Dora masa.


A lokacin da ya ke maida jawabi, Mai daraja gwamnan jahar Zamfara, Hon. (Dr.) Bello Muhammad Matawalle, ya nuna jin dadinsa Da wannan ziyara Da tsohon shugaban KASAR ya kawo masa.


"Hakika mun San irin gudunmawar da kuka bayar lokacin da kuka jagoranci, kasar nan. Musamman ta fuskar inganta walwala Da jin dadin Al'ummar Najeriya. Wanda insha Allahu za mu kokarin koyi da da ku.


"Zuwa yanzu babban abunda mu ka sanyawa, sanya a gaba. Shi ne kawo karshen matsalar tsaron jahar nan. Domin ba ranar da za mu kwanta idonmu biyu alhali rayukka da dukiyoyin al'ummarmu na salwanta. Dan haka za mu so ku bayar da duk gundumawarmu, wajen kawo karshen wannan matsalar a matsayinku na tsofaffin jami'an tsaro, da kuka San kauli-da-ba'adin matsalar tsaro.

" Dan haka a kullum kofa ta a bude ta ke GA duk Wanda zai shigo jahar Zamfara Da zummar taimaka a kawo karshen matsalar tsaron jahar. Wanda yanzu alhamdulillahi an Fara samun wasu daga cikin barayin sun Fara Mika mukamansu.


"Daga karshe muna kira ga al'ummar jahar Zamfara Da mu cigaba Da baiwa Gwamnati goyon baya, duk Wanda ya ga wani Abu Wanda bai yarda Da shi ba, to ya Kai rahotonsa ga hukuma. Haka zalika dole sai kowanenmu ya tashi tsaye wajen addu'a.


Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau 

29-6-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here