Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara, Hon (Dr) Bello Mohammed Matawalle (Matawallen Maradun) ya nemi shawarar tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soji, Janar Yakubu Gowon Domin samun hanyar da za a kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar jahar Zamfara.
Gwamnan ya yi wannan rokon ne, ga wannan Datttijo a lokacin da ya kawo masa ziyara a Gidan Gwamnatin jahar Zamfara Da ke Gusau.
Gwamna Matawalle, ya bayyana cewa kafar Gwamnatinsa a bude take, Domin neman shawarwari ga tsofaffin shuwagabannin kasar nan irin su Gowon, Da su ka yi fafutukar ganin sun kawo karshen yakin basasa a lokacinsu.
Gwamnan ya Kara Da cewa " a gogewarka da nakaltar da ka yi a bangaren sha'anin tsaro, muna neman shawararka akan hanyoyin da su ka dace mu bi Domin shawo kan matsalar tsaron da de addabar al'ummarmu"
Ya Kara da cewa irin gogewarka a matsayin tsohon shugaban kasa, kuma tsohon Janar a Rungunar sojin kasa ta Najeriya , Wanda a lokacinka ka yi kokarin samar da zaman lafiya hadin Kai Da dorewar kasar nan tsintsiya madaurinki daya.
Matawallen ya Kara Da cewa mu shuwagabanni na yanzu Najeriya muna bukatar ire-irenku. matuka gaya, Domin taimaka muna da shawarwari domin shawa kan matsalolin ta'addanci, garkuwa da mutane da kuma sauran ayukkan assha! A Najeriya baki daya.
Gwamnan ya bayyana lokacin shugabancin Gawon a matsayin lokaci mafi kalubale na matsalar tsaro, Amma gwamnan ta yi kokarin magance su, tare da kawo abubuwan cigaban kasa da dama ga al'ummar Najeriya kamar shirin ODOJI Wanda shirin ya taimaka matuka gaya wajen rage matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta a lokacin.
A kokarinsa na kawo karshen matsalar tsaron. Gwamnan ya bayyanawa tsohon shugaban kasar kokarin da Gwamnatinsa ta yi daga lokacin da ta hau kan karagar mulki zuwa yau Domin ganin an shawo kan matsalar tsaron. wanda ya hada da sulhu Wanda yanzu haka an samu gajiyarsa domin har an samu karbar bindigo sama Da 216 Kirar AK47 Na 'yan ta'addar Da su ka mika wuya tare da kokarin rungumar zaman lafiya a kasa da watanni biyu Da kafuwar wannan Gwamnatina.
Gwanna Matawalle ya Ya kuma godewa dattijon da wannan ziyara, ya kuma ba shi tabbacin cewa gwamnatinsa a shirye take ta karbi shawarwarin masana irinsa a ko ina su ke a Nigeria Domin Samar da jahar Zamfara mai yalwataccen zaman lafiya.
Tun da farko, a na sa jawabin tsohon shugaban Kasar Janar Yakubu Gowon. Ya bayyana cewa ya zo jahar Zamfara, a cigaba da rangadin Da ya ke yi a jahohin Arewa masu Yammacin Najeriya. Domin addu'a ga gwamnonin yankin, Domin samun albarka da kuma nasara a mulkinsu.
Ya Kara da cewa wannan rangadin addu'o'i kungiyar fada-fada ta Najeriya ce ta shirya shi.
Janar Gowon ya bayyana cewa addu'a ce ta dace ga dukkanin al'ummar Najeriya su cigaba Da yi Domin cigaban kasar Da dorewar zaman lafiya a kasar, Domin samun hadin kai da yalwar arziki.
Wanda su ka samu halartar zaman sun hada Da sakataren Gwamnatin jahar Zamfara Alh Bala Bello Maru, shugaban ma'aikata a fadar Gwamnati Kanal Bala Mande, Sanata Lawal Hassan Dan-Iya, Kakakin Majalissar Dokokin jahar Zamfara, Hon Nasiru Maazu Magarya da sauran Manyan jami'an Gwamnatin jahar.
YUSUF IDRIS G
Babban Daraktan Watsa Labarai a Fadar Gwamnatin Jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
30/06/2019




