Gwamna Bello Muhammad (Matawallen Maradun) ya bayyana zai daga martabar kamfanin Samar da Takin Zamani Mallakar jahar Zamfara, bayan farfado da aikinsa kwanaki Kadan da hawa mulkinsa.
Gwamnan ya bayyana haka ne, a ziyarar Gani da Ido Da ya kai a kamfanin a yau Laraba 1-7-2019. gwamnan ya kara Da cewa yana daya daga cikin manufofin Gwamnatinsa, inganta aikin wannan kamfanin ta yadda zai iya gogayyan Da takwarorinsa
Gwamna Matawalle ya bayyana cewa ya Gwamnatinsa ba ta sanya kamfanin Ido ba, bayan shafe Shekaru 13 da rufe shi. Dan haka Gwamnatinsa ta bayar da gudunmawar farko Domin jaraba aikin kamfanin Wanda ya Haifar da halin da kamfanin ya kasance a yau, inda kamfanin ya ke aiki wurjanjan.
Shugaban kamfanin, Alhaji Mustapha Muhammad ya shedawa gwamnan cewa yanzu haka kamfanin na samar da Ton 36 na taki a duk awa daya tare da samar da buhu 84,000 duk Wata.
*Zailani Bappa
SSA, Public Enlightenment, Media and Communications.
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
1-7-2019




