WAMBAN SHINKAFI YA RUBUTAWA HUKUMAR EFCC WASIKAR NEMAN TA BINCIKI TSOHON GWAMNA YARI! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 2 July 2019

WAMBAN SHINKAFI YA RUBUTAWA HUKUMAR EFCC WASIKAR NEMAN TA BINCIKI TSOHON GWAMNA YARI!


A wata zungureriyar wasika da tsohon Dan Takarar gwamnan a Karkashin tutar jam'iyar APGA ya turawa hukumar. Wadda aka tura jiya 1-7-2019

Ya bayyana cewa yana son hukumar ta binciki tsohon gwamnan, akan rahoton Da kwamitin karbar mulki ya fitar inda kwamitin ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya bar bashin Naira Biliyan dari biyu Da Hamsin Da daya Da duriya. Sai dai ta hannun Mai taimaka masa ta  bangaren Watsa Labarai sun karyata rahoton Malam Ibrahim Wakkala Wanda ya bayyana cewa sun bar kudin.

Haka zalika tsohon Dan Takarar gwamnan, ya nemi hukumar EFCC din da ta binciki Sakataren tsohon gwamnan Wanda ya shedawa duniya cewa gwamnatinsu ta kashe naira Biliyan talatin Da Biyar a matsugunnan 'yan gudun hijira na jahar Zamfara. Sai dai a Cewar Dan Takarar na jam'iyar APGA Hon. (Dr.) Sani Shinkafi. A jahar Zamfara babu sansanin 'yan gudun hijira daya tilo, Da aka kafa.

Dan haka ya nemi hukumar da ta tabbatar ta yi binciken kwakwab a cikin wannan barahira.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

2-7-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here