GWAMNATIN ZAMFARA ZA TA MIKA KUDURIN HUKUCIN KISA GA 'YAN TA'ADDA A MAJALISAR DOKOKIN JAHAR - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 12 June 2019

GWAMNATIN ZAMFARA ZA TA MIKA KUDURIN HUKUCIN KISA GA 'YAN TA'ADDA A MAJALISAR DOKOKIN JAHAR


A kokarin Gwamnan jahar Zamfara , Hon (Dr) Bello Mohammed Matawallen-Maradun na kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar Zamfara Gwamnatinsa ta Gama duk wani shiri domin Samar da dokar KISA GA duk Wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane Don karbar kudin fansa da kuma masu tallafa masu da bayanan sirri

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Talata, lokacin da ke karbar bakuncin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria a Gusau babban Birnin jahar Zamfara.

Gwamna Matawalle ya bayyana daukar wannan matakin ne a wurin bikin rantsar da 'yan Majalisar jahar Zamfara, in da ya Bayyana cewa kuduri na nan an shirya za a kawo masu zuwa ranar alhamis domin yin bitarsa domin ya zama doka.



Gwamnan ya shawarci masu aikata ta'addaci a jahar Zamfara da su mika wuya. Tare rungumar zaman lafiya. Ya kuma yi alkawarin Samar da abubuwan more rayuwa a duk Inda ruggar Fulani take

Haka zalika Gwamnan ya yi bayyana cewa zai Samar masu da tsaftatattun ruwan sha. da saurar da za su kiwata dabbobinsu  da makarantannin da 'ya'yan fulanin za su shiga. Domin babba daga cikin abubuwan da su ka kawo matsalar tsaron Zamfara shi ne matsalar rashin ilimi.

A lokacin da ya ke mayar da jawabi Shugaban Kungiyar Miyetti Allah, Alhaji Kiruwa Muhammad ya ce ya zo Gusau ne , domin taya Gwamnan jahar Zamfara nasarar da ya samu na zama Gwamna. Tare da tallafawa ta yadda za a taimaka domin kawo karshen matsalar tsaron jahar tare da Samar da zaman lafiya Mai Dorewa.

Kiruwa ya yi Kira ga Gwamnatin da kada tabar masu tada zaune tsaye su tafi hannu biyu in an yi nasarar Kama su. Dan haka a tabbatar duk Wanda aka Kama da hannu wajen yada zaune tsaye ya fuskanci hushin hukuma.

Zaman ya samu halartar mataimakin Gwamnan Zamfara Barista Mahadi Ali Gusau, Tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara , Mallam Ibrahim Wakkala Muhammad, shugaban jam'iyar PDP na jahar Zamfara , Alhaji Ibrahim Mallaha Gusau, Sakataren Gwamnatin Zamfara, Alhaji Bala Bello Maru, Daraktan yakin neman Zaben jam'iyar Matawalle a 2019, Alhaji Jamilu Aliyu Zannah, Shugaban Majalisar Sarakunan jahar Zamfara,Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad tare da dukkan shuwagabannin jami'an tsaron jahar Zamfara da sa sauran su.

YUSUF IDRIS G
Babban Darattan Watsa labarai Na Gidan Gwamnatin Jahar Zamfara
Fassara: Abdulmalik Saidu Maibiredi
11/06/2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here