"Ina godiya ga Allah subhanahu wata’ala da ya ba mu ikon hadu a wannan filin taron domin murnar ranar dimokaradiya a shekarar ta 2019. Dukkanmu mun taro a wannan fili ne domin murnar cika shekaru 20 da kafuwar mulkin dimokaradiya a Nijeriya. Hakika wannan ba karamin abun jin dadi ba ne, kuma dama ce gare mu da mu Tashi tsaye domin bunkasar dimokaradiyar ta yadda za a samu cigaba.
2. "Wannan babbar ranar Tarihi ce gare mu, ina amfani da wannan damar domin jinjina ga zakakuran gwarazanmu da su Ka yi fafutukar ganin Dorewar mulkin dimokaradiya, da su ka sadaukar da rayukkan su domin namu su inganta a mulkin dimokaradiya. Babba daga cikin wadanda su ka taka muhimmiyar rawa wajen Dorewar dimokaradiya a wannan zamani shi ne Chief Masood MKO Abiola, Wanda shi ne ya aka sauya ranar dimokaradiya daga 29-5- na kowace shelarazuwa 12-6- domin girmamawa gare shi a gwaggwarmayar da ya yi ta dawowa da kasarmu kan turbar dimokaradiya. Allah ya jikan Chief MKO Abiola, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari da sauran 'yan gwaggwarmayar kafuwar mulkin dimokaradiya.
3. "Al'umma ta jahar Zamfara, wannan ita ce ranar dimokaradiya ta farko da na sheda a matsayina na Jagoranku. Dan haka zan yi amfani da wannan damar domin Sanar da ku yunkurin da Gwamnatina ke yi domin Samar da cigaba mai Dorewa domin bunkasar jahar Zamfara, Musamman matsalar tsaro.
4. "Kamar yadda tun Bayan rantsar da ni a matsayin Gwamnan jahar Zamfara, cewa Gwamnatina za ta tashi tsaye domin 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da sauran ayukkan assha! Wanda haka ya yi sanadiyar durkushewar al'amurran jahar Zamfara Shekaru da dama baya. Dan haka 'yan kwanakin baya na gana da Shugaba Muhammadu Buhari Inda mu ka tattauna da shi akan yadda za a kawo karshen matsalar tsaron jaharmu. Wanda Tuni ya bayar da umurnin turo rundunonin jami'an tsaro na 'yan sanda biyu a Zamfara.
5. " haka zalika na tattauna da wasu manyan Jagororin jami'an tsaron kasar nan a Abuja. Tare da ziyartar tsohon Ministan tsaron Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki akan sha'anin tsaro mu ka tattauna da su akan yadda za a shawo kan matsalar ta hanyar da ta dace domin dakushe duk wani yunkuri na "yan ta'adda. Yanzu haka da na ke magana da ku mun Fara ganin alfanun wannan yunkurin na Samar da zaman lafiya a Zamfara. Ina baki tabbacin cewa a yan kwanaki kalilan masu zuwa na Gwamnatinmu za ku ga kokarin da mu ke yi na dawo da zaman lafiya a jahar nan.
6. " ina amfani da wannan damar in yi Kira masu tada gayar baya da su mika wuya domin samun zaman lafiya a jaharmu. Domin a shirye Gwamnatinmu ta ke ta canza tunanen 'yan ta'addar tare da dawo da su cikin al'umma domin samun cigaba mai dorewa.
7. " Yana daga cikin kudurorina samun Dorewar cigaban dimokaradiya, ba tare da kallo me bambancin jam'iya ko Bangaranci ba. Kullum fatana shi ne masu ruwa da tsaki da ke da gudurin ciyar da jahar gaba, su shigo domin bayar da ta su gudunmawar wajen bunkasar jahar Zamfara.
8. " Daya daga cikin manyan kudurorina su ne tallafawa sha'anin Noma. Yanzu haka na Fara yunkurin yashe dam din Bakalori domin Samar da abinci da tsaro tare da amfani da wutar lantarki ta amfani da dam din Wanda zan bunkasa masana'antu. Kari akan haka, ina sheda maku cewa shirin bunkasa noman Kwakwa Tuni ya yi Nisa hadin guiwa da masana daga kasashen ketare. Domin a makon da ya shude na ziyarci kamfanin Samar da takin zamani. Na kuma binciki halin da wurin ya ke ciki. Inda na tattauna da masu gudanar da kamfanin ta yadda za a farfado da kamfanin. Kuma ina tabbata maku nan gaba kadan za a farfado da sha'anin Noma a jahar Zamfara.
9. Mun yakar talauci a jahar Zamfara na bukatar biyar hanyoyi da dama. Wanda su ka hada da: farfado da sha'anin Noma, farfado da shirin koyawa matasa sana'o'in hannu, inganta albashi da walwalar ma'aikatan Gwamnatin jahar Zamfara, Samar da hanyoyin da Manya da kayan yan Kasuwa za su samu tallafi. Tuni dai shiri ya kamkama domin Samar da wuraren koyawa matasa sana'o'in hannu a duk fadin jahar Zamfara domin tabbatar da matasa sin samu hanyoyin dogaro da Kansu. Gwamnatina za ta maida hankali wajen Samar da hanyoyin da kasuwancin jahar Zamfara zai bunkasa. Ba zan manta ba a Shekarun baya garin Gusau. Cibiya ce ta kasuwanci, a arewacin najeriya Nigeria dama najeriya baki daya. Amma yanzu abun bakin ciki dama ban Haushi wannan ya zama tarihi. Dan haka Gwamnatina za ta yi kokarin ganin ta farfado da kasuwanci masana'antu a duk fadin jahar Zamfara.
10. A daya cikin yunkurinmu na farfado da jahar Zamfara mai albarka, Gwamnatina Tuni ta yi shiri mai kyau domin Gina filin jirgin sama a Gusau, Wanda Hakan zai faru ne ta hanyar sanya hannu jarin 'yan Kasuwa. Da za mu hada Kai da su. Domin zirga-zirga ta hanyar jirgin kasa zai habbaka Kasuwar tare da rage yawan matsalar tsaron da ke afkawa mutane masu tafiya a tituna.
11. " Mu a yarda cewa cewa mulkin dimokaradiya ba wai tana nufin Zabe ko baiwa 'yan kasa damar yin siyasa kawai ba, A'a dimokaradiya na nufin ta ya za a farfado da tattalin arziki da Samar da ababen more rayuwa ga Al'umma. Tana nufin Samar da kyakkyawan Jagoranci ta yadda za a samu zaman lafiya kwanciyar hankali da kuma cigaba.wanda wannan shi ne babbar manufar dimokaradiya a duk. dan haka ko mu kanmu ba mu da wata dauka da mu ka yi mata wadda ta wuce haka, kuma Muna kokarin Kare su.
12. " al'ummar jahar Zamfara na San za ku ji dadin mulkin dimokaradiya Idan akan Samar maku da abubuwan more rayuwa. Dimokaradiya ba wai Tana nufin zallar yunwa ta mamaye Al'ummarmu ba, a duk lokacin da Al'umma su ka kasa barci da idonsu biyu a cikin gidajensu, da kuma fadan kabilanci ya zama karfen kafa a cikin al'ummarmu Wanda ya yi hannun riga da sanadiyar samuwarmu a doron kasa. Insha Allahu Gwamnatinmu za ta yi hannun riga da wannan. Dan haka za mu yi ta kokarin ganin mun dawo da aminci da fahintar juna da ke tsakanin Hausa/Fulani, tare da zakulo matsalolin da su ka haifar da rashin fahintar juna Wanda za mu yi kokarin magance shi.
13. "Daga karshe zan yi amfani da wannan damar domin godiya ga al'ummar jahar Zamfara wadanda ke tare da mu nan da kuma wadanda ke cikin gidanjensu, akan goyon Bayan da kuke ba wannan Gwamnatin. Hakaki Muna matukar godiya ga Fatan nasarar da kuke yi Muna. Haka zalika Muna godiya da addu'o'inku da fatan alherin da ku ke yi Muna.
14. Ina yi maku barka da Bukin ranar dimokaradiya.
15. Allah ya taimaki jahar Zamfara.
16. Allah ya taimaki kasarmu Nigeria.
17. Ina godiya. Wassalamu Alaikum.
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
12-6-2019

