GWAMNA MATAWALLEN-MARADUN YA YA NUNA DAMUWARSA GA HALIN DA MAKARANTUN GWAMNATIN ZAMFARA KE CIKI. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 13 June 2019

GWAMNA MATAWALLEN-MARADUN YA YA NUNA DAMUWARSA GA HALIN DA MAKARANTUN GWAMNATIN ZAMFARA KE CIKI.


Mai daraja gwamnan jahar Zamfara Hon. (Dr) Muhammad Bello Matawallen-Maradun ya Nuna matukar damuwarsa ga halin Da makarantannin sikandire su kw ciki a jahar Zamfara.

Matawallen-Maradun  ya nuna wannan damuwar ne, ranar Laraba a ziyarar ba-za-ta da ya kai a makarantar 'Yan Mata ya  Government Girl's Unity Secondary School Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu ta jahar Zamfara.

Matawalle ya nuna damuwa matuka gaya da ganin dalibbai suna kwana kan gadon karfe ba tare da dora wani bargon kirki ba, uwa uba katifa a makarantar ''yan mata irin ta kwatarkwashi a wannan zamanin Da my ke ciki.

Ya bayyana cewa bangaren ilimi na daya daga cikin bangarorin da gwamnatinsa za ta yi kokarin farfado  da shi.

Ya kuma nuna damuwa matuka gaya da halin Da ya samu makarantar, musamman Da ya zagaya dakunan kwanan dalibbai Da ya tarar dalibbai suna kwana kan gadajen karfe babu ko katifa.

Ya cebIn Shaa Allah, zai yi gaugawar farfado Da sha'anin ilimin jahar. Domin Samar da bigeren karatu mai mai kyau Wanda zai tallafawa dalibbai su Kara hazaka.

" Tun lokacin Da na fahinci haka, da na hau kan karagar mulki na sanyawa bangaren ilimi dokar ta baci, Domin nuna danuwa ta akan matsalar tare da dawo Da martabarsa a jahar Zamfara."

Kari akan hakan gwamnan ya umurci a Samar Da Katifu 2000 ga dalibban tare da gyara dakunan kwanan dalibban da ma gyara katangar makarantar.

Gwamnan Wanda tsohon Malami ne a makarantar ya bayar Da kyautar shanu biyu ga Malamai Da dalibban makarantar.

Haha zalika gwamnan ya yi alkawarin Samar bas-bas ga dukkanin makarantannin sikandire Da ke jahar Zamfara. Domin saukakawa dalibbai damar tafiye-tafiye.

A lokacin da take jawabi shugabar makarantar, Hajiya Hauwa'u Shehu Idris ta godewa gwamnan akan wannan ziyara Da gwamnan ya kawo masu tare da bayyana ta a matsayin wani abun cigaba.

Ta Kara Da cewa wannan ziyara ta gwamnan babban abun tarihi Da makarantar ba za a taba mantawa Da ita ba a cewarta.

" Don haka a madadin dukkanin ma'aikata, da dalibban makarantar, muna godiya Da wannan ziyarar ba-za-ta da ka kawo a wannan makaranta.

" A tarihin wannan makarantar ba mu taba samun wani gwamna ya ziyarci wannan makaranta da nufin Kara muna karfin guiwa iron wannan ba. In ka debe daya a lokacin da mataimakin shugaban kasa, Prof. Yemi Osinbajo  ya zo Domin bude wasu ayukka a shekarar 2016.

YUSUF IDRIS G
Babban Daraktan Watsa Labarai A Gidan Gwamnatin Jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
12/06/2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here