Mai Daraja Gwamna, Muhammad Bello Matawallen-Maradun ya bayyana cewa Gwamnatinsa za ta zartar da hukuncin kisa ga duk Wanda aka samu da laifin tallafawa 'yan ta'adda da bayanan sirri
Gwamnan ya Sanar da haka ne a yau Lahadi lokacin da ya ziyarci Kauyen Lilo da ke Gundumar Wonaka ta karamar hukumar Gusau da ke jahar Zamfara
Gwamnan ya jajantawa Al'ummar Kauyen akan rasa rayukkan mutane takwas da su ka yi sanadiyar harin 'yan ta'adda da suka far masu jiya
Ya Kara da cewa Gwamnatinsa ba za ta zura Ido 'yan ta'adda su cigaba da cin karensu babu babbaka a jahar ba
" Za mu tura kuduri a Majalisar jahar da an Kaddamar da su. Dan haka ina ba ku tabbacin cewa kudurin dokar kashe masu bayar da sirri ga 'yan ta'addar zai samu amincewarsu. Kuma za mu aiwatar da kisan ga duk Wanda aka samu da hannu wajen tallafawa ta'addanci.
" Haka kuma 'yan sa-kai su guji daukar doka da hannunsu. Domin Gwamnatinmu ba za ta aminta da Hakan ba.
" A Matsayinka na Dan sa-kai ba ka da hurumin kisan kowa duk laifin da ya yi. Dan haka daga yau an kawo karshen wani Dan sa-kai ya kashe wani.
"Abun bakin ciki ne, irin yadda ake kisan al'ummarmu ya zama ruwan dare game duniya. Domin Bayan na zama Gwamnan Zamfara na tarar da Mummunar matsalar tsaro. Duk da ba zamfara kurrum ta tsaya ba da sauran lungu da sako na kasarmu.
"Idan aka Kama Dan ta'adda, ku hannunta shi ga hukuma. Akwai kyakkyawan tsari da Gwamnatinmu ta yi domin magance matsalar da ke addabarmu. Abunda kawai mu ke fata shi ne ku taya mu da addu'a".
"Gwamnatinmu ta tanadi kayan Aiki da hanyoyin sadarwa da za a yi amfani da su wajen taimakawa jami'an tsaro su yi aikinsu cikin natsuwa.
" Jami'an tsaro na sanya ido ga duk Kiran wayar da ake yi a jahar Zamfara. Dan haka ina kira ga 'yan ta'adda da su mika wuya ko su fuskanci hushin hukuma.
Tun da farko dai Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau Alhaji Ibrahim Bello ya gode wa Gwamnan a wannan ziyara da ya, tare da Kira ga Gwamnatinsa da ta Kara baiwa bangaren tsaro muhimmanci domin kawo karshen kashe-kashen rayukka da dukiyoyin al'umma.
Matawallen na Maradun ya roki al'umma da su Tashi tsaye wajen taimakawa gwamnati da addu'a domin samun nasarar kawar da ta'addanci a Zamfara
Gwamnan ya bayar da tallafin naira Miliyan biyar ga Iyalan Wanda dinka rasa rayukkansu tare da umurtar Sakataren Gwamnati da a dauki nauyin samawa dukkanin wadanda suka Jikka magani.
Yusuf Idris G
Director press Affairs
Government House, Gusau.
Fassara: Abdulmalik Saidu Maibiredi

