Gwamnan jihar zamfara, Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya bayyana cewa daga yau, gwamnatinsa ta sauya tsarin biyan albashin ma'aikatar a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen rantsar da sabon sakataren gwamnatin jahar .
Gwamnan ya ce daga yanzu tsarin biyan albashin zai tashi daga ma'aikatar kudi zuwa. ma'aikatun gwamnati.
Ya Kara da cewa kowace ma'aikata ita za ta rika biyan albashin ma'aikatanta, ya Kara da cewa Ka da wani sakataren ma'aikata ya nufi shi dauke file, sai dai a kai shi ofishin sakataren gwamnatin jaha domin shi ke da alhakin haka.
Haka zalika Gwamnan ya bukaci kowane ma'aikaci ya maida hankali kan aikinsa, Wanda ba zai iya aiki ba to ya koma gida ya zauna.
Daga karshe ya bukaci sakataren gwamnatin da ya yi aiki wurjanjan in da dama ma ya dauki dabi'ar zagayawa a ma'aikatu domin duba yadda ma'aikata suke zuwa aiki.

