GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA ZA TA INGANTA RAYUWAR 'YAN GUDUN HIJIRA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 3 June 2019

GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA ZA TA INGANTA RAYUWAR 'YAN GUDUN HIJIRA.


Gwamnan jahar Zamfara da Hon. (Dr) Muhammad Bello Matawallen Maradun zai Samar da matsugunan 'yan gudun Hijira. Domin inganta walwalarsu.

Matawallen Maradun ya bayyana haka ne a ranar lahadi lokacin da ya ziyarci sansanin yan gudun Hijira da ke garin Mada a karamar hukumar Gusau.


Bayan ya dawo daga garin Lilo Inda ya Kai ziyarar jajantawa ga al'ummar garin da 'yan bindiga suka farwa a ranar Assabar din da ta shude.


Gwamnan ya nuna samuwarsa matuka gaya ga halin da ya ga 'yan gudun Hijirar na ciki. In ya ya yi alkawarin cewa Gwamnatinsa ba za ta zura masu Ido haka ba.


" Akwai matukar Damuwa da yadda yan ta'adda ke farwa Al'ummarmu. Kamar yadda mu ka zo kan karagar mulki mu ka tarar da mummunan matsalar tsaro.

"Hakika mun damu matuka ga yadda yan ta'adda suka sa kuka rasa matsugunanku. Kuma ban ji dadi da na ga kuna cikin wannan halin ba. Dan haka za mu yi kokarin inganta rayuwarku.

" Dan na bayar da umurnin a gaggauta, Samar maku da Assibiti a nan Mada tare da samar magani kyauta domin inganta lafiyarku."

Haka zalika Gwamnan ya bayar tallafin naira 500,000 ga 'yan gudun Hijirar tare da umurnin a Samar masu sa Katifu 200 gare su.

Tare da yin Kira Al'umma Musamman masu hannu da Shuninmu da su Tashi tsaye wajen tallafawa yan gudun Hijirar.

Daga karshe ya roki Al'umma da tallafawa Gwamnatinsa da addu'a domin samun nasara.

Yusuf Idris G
Director-General Press Affairs
Governor House Gusau
Fassara: Abdulmalik Saidu Maibiredi

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here