A cigaba yunkurin na tuntubar masu masu ruwa da tsaki akan harkar tsaron Nijeriya da ma masa harkar tsaron. Gwamna Bello Muhammad Matawalle (Matawallen Maradun) ya ziyarci tsohon Ministan tsaron Nijeriya Janar Mansur Dan-Ali (mai Ritaya) a gidansa da ke Asokoro a Abuja.
Gwamnan ya ziyarci tsohon Ministan ne domin neman shawara akan hanyoyin da ya dace a bi domin magance matsalar tsaron da ke addabar Zamfara.
Gwamnan ya ziyarci tsohon Janar din sojin ne saboda zamansa Bazamfare kuma daya daga cikin manyan jahar da su ka San kauli-da-ba-adin hanyoyin da za a Samar da tsaro a jahar da kuma kishin jahar.
Gwamna Matawalle ya dauki Samar da tsaro a matsayin wani muhimmin abun da gwamnatinsa za ta a gaba. Dan Hakan za ta cigaba da yakar yan ta'adda da duk wasu masu aika ba daidai ba a cikin jahar.
A lokacin da ministan ya ke maida jawabi, ya godewa Gwamnan na nuna 'yan uwantaka da Gwamnan ya yi masa, ya kuma yi alkawarin zai taimakawa gwamnatin a yunkurinta na yakar yan ta'adda da ke addabar jahar.
Haka zalika ya jinjinawa Gwamnan a yunkurinsa na Samar da tsaron rayukka da dukiyoyin al'ummar jahar Zamfara.
Yusuf Idris G
Babban darattan Watsa labarai na gidan Gwamnatin jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Maibiredi

