GWAMNA BELLO MATAWALLE YA NUNA MATUKAR DAMUWA GA YADDA AKA WALAKANTA KAYAN GWAMNATIN ZAMFARA  - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 11 June 2019

GWAMNA BELLO MATAWALLE YA NUNA MATUKAR DAMUWA GA YADDA AKA WALAKANTA KAYAN GWAMNATIN ZAMFARA 


Gwamnan jahar Zamfara Hon (Dr) Bello Mohammed Matawalle (Matawallen Maradun) ya nuna damuwarsa da akan yadda aka bar kaddarorin Gwamnatin jahar Zamfara su ka lalace ta hanyar nuna masu halin ko-in-kula.


Gwamnan ya nuna damuwar tasa ne, lokacin da ya ziyarci masaukin baki na Gwamnatin jahar Zamfara da ke Kaduna. Wanda ya tarar duk ya lalace. Inda nan take ya bayar da umurnin a gyara, duk Inda ke bukatar gyara.

Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa dukkan ma'aikatan gidan cewa. Babban gudurin gwamnatinsa shi ne inganta jin dadi da walwalar ma'aikatan Zamfara.

Gwamna Matawalle ya yi Kira ga daukacin ma'aikatan gidan Gwamnatin da ke Kaduna da su sadaukar da Kansu wajen sauke nauyin da ke wuyansu da kuma tallafawa daidai iyawarsu wajen gina sabuwar jahar Zamfara.

Gwamnan ya Kara da cewa Sabon tsarin gyaran gidan zai kasance na zamani da zai yi zozo da takwarorinsa.  Ta yadda zai zamo wani waje da jami'an gwamnati za su samu wurin tattaunawa da ma yin taro duk lokacin da Hakan bukatar yin Hakan tusgo. Ta hanyar gayyato masu zuba jari na cikin da wajen kasar nan.

A lokacin da ya ke jawabi mai Kula da gidan Gwamnatin. Alh Mustapha Rafi Gummi. Ya bayyana cewa ba wani tallafi da gidan ya samu domin gyaransa, musamman a Shekaru takwas da su ka wuce baya.

YUSUF IDRIS G
Babban Darattan Watsa Labarai a Gidan Gwamnatin jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Maibiredi.
11/06/2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here