Shugaba Muhammad Buhari ya jinjinawa Gwamnan jahar Zamfara Hon (Dr) Bello Mohammed Matawalle (Matawallen Maradun) akan kokarinsa na daukar matakin kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara
Shugaban ya yi wannan jawabin ne, a lokacin da ya ke karbar bakuncin shuwagabannin wata Kungiya Mai suna "concerned Zamfara State citizens" karkashin Jagorancin Mallam Usman Balarabe wadanda suka ziyarci shugaba Buharin a fadar Shugaban kasa, Abuja.
Da ya ke jawabi Shugaba Muhammad Buhari ya ce " Hakika ina jin dadi ga Matakan da na ga Sabon zababben Gwamnan jahar Zamfara ya na dauka. Wanda su ka hada da zakulo Sarakunan Gargajiya da ba su yin aikinsu kamar yadda ya dace, tare da daukar matakin da ya dace da Kansu."
Shugaban ya Kara da cewa matakin da Gwamnan ke dauka zai tallafa wajen kawo karshen matsalar tsaron jahar. Dan haka al'ummarmu da sauran masu dauke da sarautun Gargajiya ya zama dole gare su da su Tashi tsaye domin sauke nauyin da ke wuyansu. In kuma ba haka ba su hadu hushin hukuma.
Haka zalika ya Kai yi alkawarin tallafawa Gwamnatin domin ganin an kawo karshen matsalar tsaron jahar dama Najeriya baki daya
Shugaba Buhari ya sheda wa shuwagabannin Kungiyar cewa a Gwamnatinsa ta riga ta tanadi dukkanin jami'an tsaron da su ka dace domin turawa a jahar Zamfara " Mun tanadi jami'an tsaro jajirtattu da Sahihan manyan jami'an tsaro da za a rinka Sanar da su duk Inda aka samu rahoton tada zaune tsaye. domin tabbatar da cewa jami'an tsaron da aka jibge sun yi aiki a duk Inda ake samun tada zaune tsaye
Shugabannin Kungiyar Zamfara State concerned citizens. Da su ka samu halartar wannan tattaunar sun hada da: Kadiria Ahmed, Mallam Usman Balarabe, Prof Yahaya Zakari, Barr Fatima Nahuche, Gazali Shehu Ahmad da Barr Mohammed Babangida Umar.
YUSUF IDRIS G
Babban Darattan Watsa labarai na Gidan Gwamnatin jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Maibiredi
10/06/2019

