ROSHEWAR GWAMNATIN APC A ZAMFARA. WA'AZI NE GA 'YAN SIYASAR NAJERIYA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Sunday, 2 June 2019

ROSHEWAR GWAMNATIN APC A ZAMFARA. WA'AZI NE GA 'YAN SIYASAR NAJERIYA.


A Najeriya kaf ba ni tunanen akwai jahar da aka taɓa, nunawa ɗan siyasa ƙauna tare da fitowa a Zaɓe shi da dukkanin ƙarfin ƙuri'a, kamar yadda aka yiwa Gwamna Abdul'azizu Abubakar Yari na jahar Zamfara. Domin Talakawan jahar sun kayar da Gwamnati Mai ci ne ta Mamuda Aliyu Shinkafi Wanda ke neman a Zabe shi Zango na biyu a karkashin tutar jam'iyar PDP wadda a lokacin ita ce jam'iya mai mulkin Najeriya. Amma ƙiri-ƙiri talakawan jahar Zamfara mu ka nuna Shehi mu ke so, mu ka ƙyamaci kuɗi da barazana iri-iri daga Gwamnati Mai ci, a lokacin.

Cikin ikon Allah ya yi nasara da gagarumin rinjaye tare da kafa Gwamnati cikin Yardar  Allah. Gwamnati Mai cike da buƙatun talakawa da fata na gari daga gare sa!

Cikin nasara ya fara mulki ɗaukaka ta Allah ya yi masa Gwamnan Gwamnonin Nijeriya. Wanda ke nuna ya sa mu dama da faɗa a ji a Nijeriya fiye da yadda sauran Gwamnonin Nijeriya su ke da ita.

Sai dai kash! Abun mamaki sai ya ɗauki rayuwa ta ko-inkula ya ɗorawa kansa. Abunda ya so shi ne daidai Wanda bai so, kuma komi kyawonsa, to jaɓa ta fishi muni a idonsa. Dan haka shawarar kowa bai ɗauka. Ba wani mahaluki a jahar Zamfara da ke iya nufar Shehi ya nusar shi wata Illa. Hasalima ganin Gwamnan tamkar gwal! Ya ke ga su kansu maƙaraban Gwamnatin. Uwa uba talakawan jahar Zamfara. Balantana a zo Maganar kula da rayuwar Al'umma. Kwata-kwata rayukkan al'ummar Zamfara sun tarwatsa, sha'anin ilimi, kiyon lafiya, walwala, Noma da kusan komi ya lalace. Uwa uba matsalar rashin tsaro da ya sa jahar ta zamarwa jahar ƙarfin-ƙafa, har aka wayi gari kullum sai an kashe, an sace ko an yiwa mata fyaɗe a lungu da saƙo na jahar Zamfara.

Amma duk haka bai sa ya zauna ya ga ina matsalar take ba. Hasalima kullum yana cikin yawon da za mu iya kira na tamɓele domin ba wani alfanu da yawon ya yi wa talakan Zamfara, kasancewar tun da ya hau ba mu ga wani aiki da za a ce ya yi da sunan haɗin guiwa tsakanin Gwamnatin Zamfara da ta wata ƙasa, ko wani kamfani da jawo daga wata ƙasa  ba. Sai da aka wayi gari Gwamna Yari na iya kwashe watanni biyu bai kwana gidan Gwamnatin Zamfara sau uku ba. Kullum yana cikin gira-gizzai, daga wannan ƙasa zuwa waccen. Wanda har aka wayi gari wata rana da aka tambaye shi ganin matsalolin da jahar ke fuskanta sun yi yawa, Amma a wayi gari Jagoranta, bai zaune, ko ya zai iya Jagorancin jahar?  Sai ya ce; shi ko a cikin jirgi zai iya Jagoranci. Wannan kenan.

Rosasshiyar gwamnatin jahar Zamfara kwata-kwata ba ruwanta da matsalar tsaron jahar, waya Allah ya yi Ƙoƙarin ganin an magance ta, domin ba zan manta ba shekarar 2016 da shugaba Buhari ya zo jahar Zamfara akan matsalar jahar, huɓɓasar Senator Ɗansadu ce, haka zalika a cikin wannan shekarar da shugaban ya ce tak! Kan matsalar, huɓɓasar ƙungiyoyin farar hulla ne da su yi ta zanga-zanga har a birnin Londo. Hatta jaje talakkan jahar Zamfara bai da kimar da za a yi masa daga Gwamna Shehi.

Wanda tarin matsalolin da ke fuskantar jahar ya sa kwata-kwata kima da martabarsa ta zube warwas a idon talakan zamfara!

Kwatsam! Lokacin zaɓe na ƙarasowa, ya shiga ɗaki, ya tsaro zungureriyar takarda, ɗauke da waɗanda ya ke son ya su gaje shi, tare da sauran dukkanin wasu muƙamai. Ya naɗa waɗanda ya ke son su yi mashi takara a ƙarkashin tutar jam'iyar APC. Tare da shi kansa da ya Kai a matsayin Wanda zai yi takarar Sanata.

Abun mamaki ita wannan takarda cike take da tarin mutane da tsantsar son rai ne kurrum zai kai su kan karagar mulki ba wai dan sun cancanta ba. Tare da watsar da wasu ƙusoshi a jam'iyar APC dama jahar baki ɗaya, da sunan kawo ƙarshen damawa da su a fagen siyasa. Kamar mataimakin Gwamna, Sanata Mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Ministan tsaron Nijeriya da dan Majalissa mai wakiltar Birnin Magaji da Ƙaura Namoda da tsohon Gwamnan Zamfara da sauransu. Kuma dukkaninsu takarar Gwamna su ke yi kuma ya yi masu ƙaryar da yardarsu ya yi hakan. Wanda Hakan ne ya fusata su, Dan haka sai su ka zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya da su ka Kira kansu da sunan G8. Waɗanda su ka sha alwashin ganin ƙarshen mulkinsa kamar yada ya so gare su. Kuma aka haɗa da talakawan Zamfara na son su, shi kuma an gaji da shi dama duk wani Abu da ya zo da shi. Hakan kuma ne ya sa Duk wani yunƙuri nasa bai yin nasara.

Domin talakan Zamfara ya ta shi tsaye da addu'a, ba dare ba Rana. Ta hanyar roƙon Allah ya tarwatsa duk wani shiri na shi. Dan haka da tun farko jam'iyar APC ta ƙasa ta sanya jahar Zamfara cikin jerin jahohin da za su yi zaɓen fitar da gwani a tsarin 'yar-tike. Wanda ya baiwa duk wani ɗan jam'iyar APC damar shiga zaben. Tabbas Hakan ya takawa Shehi burki matuƙar gaske domin ya so ya yi son ransa ta hanyar amfani da ƙarfin mulki, kuɗi da kuma jami'an tsaro. Sai dai taron talakawa su ka Hana a yi masu sakkiyar da ba ruwa. Ta hanyar Hana duk wani yunƙuri na tabka maguɗi Wanda ya yi amfani da 'yan ta'adda su ka tarwatsa runfunan Zaɓe, abunda ya Hana a samu nasarar yin zaɓen Kashi na ɗaya da na biyu kenan, daga ƙarshe ya shirya farfagandar wai ya yi Zaɓen fitar da gwani. Duk da duniya da su Kansu kwamitocin da aka turo sun Sanar da duniya ba a yi zaɓen ba, a jahar.

Wanda Hakan ne ya sa hukumar zaɓe ƙin karɓar 'yan takarar Zamfara baki ɗaya na jam'iyar APC saboda rashin gudanar da zaɓen fitar da gwani. Daga ƙarshe ya yi amfani da wasu ɓara gurbi  sashen shari'a aka yi masa abunda ya ke so. Sai dai da ya ke Allah ba azzalumin kowa ba ne kuma baya zalunci Bayan 'yan takarar Gwamna su takwas sun ɗaukaka ƙara, aka soke damar da kotu ta ba shi na sanya ƴan takararsa da har sun ci zaɓe. Bayan an yi zaben da ya yi amfani da miyagun kuɗaɗen al'umma da aiki da 'yan ta'adda da ma ɓaragurbin jami'an tsaro.

Duk da haka ya yi hayar manyan lauyoyi dan su halatta, Haram a kotun kolin Najeriya. Sai dai ranar 24-5-2019 da gagarumin rinjaye alkalai biyar na kotun ƙolin Najeriya su ka tabbatar da rashin gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam'iyar APC a Zamfara. Wanda ya nuna kenan ba ta da huromin shiga zaɓen baki daya. Dan haka kotun ta ce kuri'un da aka jefawa jam'iya na banza ne. Hakan ya sa aka baiwa waɗanda su ka yi na biyu a dukkanin kujerun da aka yi takarar su. Tun daga Gwamna har na Majalisar tarayya da na jaha. Dan haka aka wayi gari jam'iyar APC ta rasa dukkanin wani muƙami a jahar Zamfara.


Haƙiƙa akwai matuƙar abun koyi a cikin wannan balahirar.

Da farko girman kai da nuna isa da ƙoƙarin rufewa wani hanyar abinci, son Kai, haɗama, da nuna ni dai na iya da rashin ɗaukar shawara da nuna halin ko in Kula ne muraran suka tarwatsa duk wani shiri na APCn Zamfara, ƙarkashin jagorancin tsohon gwamna Abdul'azizu Abubakar Yari. Domin Wallahi da ba dan waɗancen ababen da na zayyana a sama ba ko da mafarki wata jam'iya ba ta cin Zaɓe a Zamfara, a 2019 ba. Kasancewar a shekarar ba wata rawa da jam'iyun adawa su ka taka da har za ta sa su ci zaɓe.

Amma da ya ɗauko halin ko-in-kula ga Talaka dan ya ga ya Tara abun duniya da mulki, sai Talaka ya nuna masa yana da Allah, kuma zai iya masa, cikin ikon Allah din kuma Allah ya isarwa gwamnatinsa a Zamfara ta hanyar roshe shirin mulkin mallakar da aka so a cigaba da yiwa zamfarawa. Alhamdulillahi addu'ar Talaka ta karɓu. Yanzu tsohon gwamnan gwamnonin Nijeriya, tsohon gwamnan jahar zamfara Abdulazizu Abubakar Yari da duk wani da ya Mara masa baya a 2019 ya zama Dan Kallo a siyasar jahar Zamfara. Wanda da wahala su Kara tasiri a jahar baki ɗaya. Tabbas Wannan babban Wa'azi ne ga sauran yan siyasa da mulki ke ruɗarsu su bar Talaka su koma yin son ransu.


Allah muna roƙonka wannan sabuwar Gwamnatin da ka zaɓa muna ka ba ta ikon gwara taɓargazar da wadda ta gada da ta yi. Allah ka kawo Muna zaman lafiya Mai ɗorewa da yarwar arziki a jahar Zamfara Da Nigeria baki ɗaya.


Abdulmalik  Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasan Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

28-9-1440
2-6-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here