SEN. ALU WAMAKKO YA ZIYARCI Dr. ABDULAZIZ YARI ABUBAKAR. DOMIN JAJANTA MASA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Sunday, 2 June 2019

SEN. ALU WAMAKKO YA ZIYARCI Dr. ABDULAZIZ YARI ABUBAKAR. DOMIN JAJANTA MASA!



Ayau Senator Aliyu Magatakarda Wamakko ya ziyarci Gwamna Dr. Abdulaziz Yari Abubakar domin jajantawa ga 'ya'yan jamiyar APC ta zamfara bisa abunda ya faru na cin amana daga bangarori daban-daban na abukanin hulda.

Sen. Aliyu yace babu wani abun cewa domin Kotu ce tayi abun da tayi, amma duk da haka baza'a hana Dan Uwa ya cema Dan Uwansa Hoo! Ba.

Shima Dr. Abdulaziz Yari ya bayyana abunda ya faru a zamfara na kar6ar shugabancin APC zuwa ga PDP, inda ya bayyana cewa wannan Hukunci na ubangijine kuma ya kaddara hakan zata faru tun shekaru dubu hamsin kafin halittar Sammai da Kassai. Dan haka Allah ya na jarabtar bayinsa daidai Gwargwadon imaninsu.

Hakama, Dr. Abdulaziz ya bayyana hukuncin kotun Koli Najeriya da wani abun cece kuce daga masana shari'a na gida da waje, inda suke bayyana wannan a matsayin cin amana da zalunci.

Bisa wannan Gwamna Abdulaziz Yace munbarma Allah, tareda raja'i cewa Allah zai kawo ayarsa nan bada jimawaba. Sannan daga bisani Ya godema Sen. Aliyu Wamakko bisa zanbiyarsa tareda tawagarsa.

Daga karshe, Anyi addu'o'i na musamman domin Neman Allah S.W ya cigaba da tsare Alummar da shugabancin Jimiyar APC ta Zamfara da Sokoto.

Limanchi

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here