A yunkurinta na bunkasa jin dadi da walwalar al'ummarta gwamnatin jahar Zamfara ta ware Naira Miliyan 85 domin sawo shanun rarraba ga al'ummar jahar domin saukaka masu da sanya su cikin annashawa a lokacin bikin sallah karama .
Tuni dai Mai daraja Gwamnan jahar Zamfara Hon (Dr) Muhammad Bello Matawallen-Maradun ya bayar da umurnin bayar da wadannan kudaden domin sayen shanun wadanda za a raba ga bangarori daban na mabukata a jahar Zamfara.
Wannan na daga cikin yunkurin Gwamnati domin bunkasa walwala da jindadin al'ummar jahar Zamfara
Rarrabar za ta kasance ne a tsakanin bangaren tsare-tsaren gidan Gwamnatin Zamfara da ma'aikatar lamuran aaddini ta jahar Zamfara
Gwamnan ya yi Kira ga al'ummar jahar Zamfara musamman masu hannu da Shuninmu da su Tashi tsaye wajen tallafawa 'Yan gudun Hijira, Marayu, Zawarawa da masu Dan karamin karfi da ke zagaye da su domin tallafawa cigaban jahar Zamfara.
Haka zalika Matawallen-Maradun ya yi Kira ga al'ummar jahar Zamfara da su yi amfani da wannan watan na Ramadan da lokacin bukukuwan sallah domin rokawa jahar Zamfara samun dawamammen zaman lafiya da bunkasa jahar
Yusuf Idris G
Director Press Affairs
Government House Gusau.

