GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA TA YI NASARAR KARBO MUTUM 25 A HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANE. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 4 July 2019

GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA TA YI NASARAR KARBO MUTUM 25 A HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANE.


A cigaba da yunkurin sabuwar Gwamnatin jahar Zamfara na kawo karshen matsalar ta'addanci, garkuwa da mutane dan karbar kudin fansa da kuma kawo karshen satar shanu. Ta hanyar hanyar da Gwamnatin jahar ta dauka na sulhu, ya sa an san samu nasarar sakin Fulani 25 Da 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su tun ranar 9-6-2019. Yan ta'addar sun mika wadanda su ka yi garkuwa a hannun 'yan banga wadanda aka fi sani 'Yan sa-kai. A gudunmar Dansadau ta karamar hukumar mulkin Maru da ke jahar Zamfara.

Mutum 25 din aka Mikawa 'yan sa-kai sun hada da Maza, Mata, Da kuma Yara kanana, an mika su ga Mai daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Mohammed Matawalle da kwamishinan 'yan sanda na jahar Zamfara  Mista. Usman Nagoggo a fadar Gwamnatin jahar Zamfara da ke Gusau.

A lokacin da ya ke karbar wadanda aka yi garkuwa da su din , Gwamna Matawalle, ya nuna matukar jin dadinsa ga jami'an tsaro na 'yan sanda akan goyon bayan da su ke baiwa jahar, a yunkurinsa na dawo da jahar kan turbar zaman lafiya. ya kuma nemi su cigaba da aiki tukuru, Domin samun tsaron jahar.

A lokacin da ya ke jawabi ga wadanda aka yi garkuwa da su din. Gwamna Matawalle ya taya wadanda aka yi garkuwar da su murnar samun yancinsu. Ya kuma shawarce su, da su rungumi zaman lafiya ta hanyar marawa shirin Gwamnatin jahar Zamfara Domin samun zaman lafiya Mai dorewa a jahar Zamfara Da Najeriya baki daya.

Haka zalika gwamnan Ya nemi Fulani Da su shawarci, al'ummarsu da sauran al'ummar da su ka rungumi sulhu Domin samun zaman lafiya.

Gwamna Matawalle Ya kuma nemi al'ummar jahar Zamfara Da tallafawa Gwamnatinsa Domin kawo karshen matsalar tsaron jahar.  Domin Al'umma su dawo daga cikin hayacinsu ba tare da tsoro ko fargaba ba.

Matawalle ya Umurci a yi kokarin saita tunanen wadanda aka saki din Kafin kowa da su a cikin iyalansu, domin su cigaba da rayuwa kamar yadda su ka Saba.

 YUSUF IDRIS G

Babban Daraktan Watsa Labarai A Fadar Gwamnatin Jahar Zamfara.

Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

04/07/2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here