HUKUMAR EFCC TA KARBI TAKARDUN WAMBAN SHINKAFI YA RUBUTA MATA NA NEMAN TA BINCIKI TSOHON GWAMNAN JAHAR ZAMFARA ABDUL'AZIZU YARI! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 5 July 2019

HUKUMAR EFCC TA KARBI TAKARDUN WAMBAN SHINKAFI YA RUBUTA MATA NA NEMAN TA BINCIKI TSOHON GWAMNAN JAHAR ZAMFARA ABDUL'AZIZU YARI!







Daya daga cikin masu kishin jahar Zamfara, kuma tsohon Dan Takarar gwamnan a Karkashin tutar jam'iyar APGA ALH. Dr. *Sani Abdullahi Shinkafi,* ya Kara rubutawa hukumar YAKI da cin Hanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa ta Najeriya (EFCC) Wata zungureriyar wasika, inda ya nemi hukumar ta binciki tsohon gwamnan akan almubazaranci Da dukiyar al'ummar jahar Zamfara a lokacin mulkinsa na Shekaru takwas.


TUHUMCE-TUHUMCEN dai sun hada da da


1- Naira BBiliyan ashirin da biyar (25, 000,000,000:00) Da aka baiwa wani kamfani Mallakar  Abba Aleiro da sunan sanya wuta a kananan hukumomi 14. Ba tare da an bi hanyar da ta dace wajen bayar da kwangilar ba, Wanda haka ya sabawa tanadin dokar bayar da kwangila ta Shekara 2007. Haka zalika kamfanin ba shi da karfi da MA kwarewar yin aikin da kamfanin ya ke Da ita. Kari akan hakan har yanzu kamfanin bai Kammala Kashi 30 cikin 100 na aikin ba. Kuma an yi amfani da kayan da aiki Marar inganci wajen aikin.


Dan haka ya yi Kira ga hukumar da ta shigo cikin wannan barahira ta hanyar bincikar yadda aka biya kamfanin naira Biliyan ashirin (N20,000,000,000; 00) a asusun Gwamnatin jahar Zamfara duk da ba a Kammala aikin ba..



2. Haka zalika ya yi Kira ga Hukumar ta binciki Abdulaziz Yari akan yadda ya yi ta amfani da dukiyar jahar Zamfara yana daukar shatar jirgin kasaita a duk mako naira miliyan goma ( N10,000,000,000) makonni 56 a hadi Da Shekaru 8 akan kudi naira Biliyan hudu da miliyan dari hudu Da tamanin (N4.480,000,000,000 ) baya ga tafiye-tafiye da ya yi ta yi a kasashen Saudi Arabia, Dubai, China, Europe da America da sauransu. Wanda in aka hada Hancin kudin za su Kai Biliyan uku. Amma a Shekaru takwas ba tare da ya gayyato ko da masu sanya hannun jari daya daga kasashen ketaren zuwa jahar Zamfara ba.


3. Tumuha ta uku ita ce bincikar yadda tsohon gwamnan ya bayar da kwangilar Kai kwai fa GA dalibban sikandire har naira miliyan arba'in (N40,000,000:00) duk wata ga kamfanin Rufai Farms Mallakar tsohon gwamnan jahar Zamfara Sanata Ahmed Sani (Yariman Bakura ).  Duk Wata miliyan arba'in. (N 40 Million) in hada Watanni sha biyu sau takwas kudin sun Kama= naira Biliyan uku da miliyan dari takwas Da arba'in (N3.840,000,000:00) Wanda aka baiwa tsohon gwamnan Kai tsaye a fitar duk Wata zuwa ga kamfanin har a cikin watannin Hutu. dan haka hukumar ta bincike akai.



4 Tumuha ta uku ita ce zargin yadda gwamnan ya bayar da kwangilar gina tituna a kananan hukumomi 14 akan naira Biliyan saba'in da biyar ba tare da biyar dokokin bayar da kwangilar ta 2007 ga kamfanin da ya yi kwangilar ba. Haka zalika, zuwa yanzu wasu ayukkan har yanzu ba su Kammala ba, Amma an biya sama da Kashi 80 cikin dari na kudin ga kamfanonin Da su ka yi aiki.



5. Tuhuma ta biyar ita ce wamban na Shinkafi yana son a binciki yadda tsohuwar gwamnatin ta kashe naira naira Biliyan biyu da sunan Zaben kananan hukumomi a cikin kwanaki goma na karshen mulkin Gwamnatinsa

Wannan takarda dai wamban na rubuta ta a jiya Alhamis 4-7-2019 yau Jumu'a hukumar ta EFCC TA karbi takardun.


Fassara: *Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau*


5-7-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here