A cigaba da yunkurin sabuwar Gwamnatin jahar Zamfara na kawo karshen matsalar ta'addanci, garkuwa da mutane dan karbar kudin fansa da kuma kawo karshen satar shanu. Ta hanyar hanyar da Gwamnatin jahar ta dauka na sulhu, ya sa an san samu nasarar sakin mutane 15 Da 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su a hanyar Kaura Namoda ,Zurmi da kuma Shinkafi, mutanen Da suka hada da maza 13 Mata 2
Mutum 15 din, an mika su ga Mai daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Mohammed Matawalle da kwamishinan 'yan sanda na jahar Zamfara Mista. Usman Nagoggo a fadar Gwamnatin jahar Zamfara da ke Gusau.
A lokacin da ya ke karbar wadanda aka yi garkuwa da su din , Gwamna Matawalle, ya nuna matukar jin dadinsa ga jami'an tsaro na 'yan sanda akan goyon bayan da su ke baiwa jahar, a yunkurinsa na dawo da jahar kan turbar zaman lafiya. ya kuma nemi su cigaba da aiki tukuru, Domin samun tsaron jahar.
A lokacin da ya ke jawabi ga wadanda aka yi garkuwa da su din. Gwamna Matawalle ya taya wadanda aka yi garkuwar da su murnar samun yancinsu. Ya kuma shawarce su, da su rungumi zaman lafiya ta hanyar marawa shirin Gwamnatin jahar Zamfara Domin samun zaman lafiya Mai dorewa a jahar Zamfara Da Najeriya baki daya.
Gwamnan ya bayar da umurni ga jami'an kiyon lafiya, da su duba lafiyar wadanda aka sako din Kafin Mika su ga iyalansu.
Cikin wadanda aka sako din akwai mutum daya Haruna Na-hantsi Dan kasar Janhuriyar Nijar ne. Sai Ibrahim Muhammad Moriki Wanda ma'aikacin kiyon lafiya ne, da ke aiki da karamar Assibitin shan Magani ta Katuru, Wanda masu garkuwan su ka yi garkuwa Da shi kwanaki 20 baya. Sauran kuma sun kwashe sama da watanni biyu a hannun masu garkuwar
Gwamna Matawalle Ya kuma nemi al'ummar jahar Zamfara Da tallafawa Gwamnatinsa Domin kawo karshen matsalar tsaron jahar. Domin Al'umma su dawo daga cikin hayacinsu ba tare da tsoro ko fargaba ba.
Matawalle ya Umurci a yi kokarin saita tunanen wadanda aka saki din Kafin kowa da su a cikin iyalansu, domin su cigaba da rayuwa kamar yadda su ka Saba.
Wadanda su ka kubuta din, sun bayyana cewa an sake su ne a wani gari Mai suna kagara Da ke karamar hukumar Isa ta jahar Sokoto. Daga nan ne aka dauko su zuwa fadar Gwamnatin jahar Zamfara
YUSUF IDRIS G
Babban Daraktan Watsa Labarai A Fadar Gwamnatin Jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
05/07/2019




