CIGABA DA GININ JAMI'AR JAHAR ZAMFARA, BA TAIMAKAWA ZAMFARAWA BA NE! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 11 July 2019

CIGABA DA GININ JAMI'AR JAHAR ZAMFARA, BA TAIMAKAWA ZAMFARAWA BA NE!



Mai Karatu zan so ka natsu ka karanta abunda na rubuta, Kafin ka yi mini comments ko yadda maganar gaba!

A duk fadin Nijeriya ba babu jahar da ba ta da jami'a mallakarta, sai jaharmu. Hasalima ita kanta jami'ar Tarayya da ke Gusau, an assasata Shekaru biyar baya, lokacin jagorancin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. A 2013.

Wanda kafa wannan jami'ar ya sa da dama daga cikin al'ummar jahar Zamfara mu ke cigaba da cin gajiyarta, Wanda ni kaina ina daga cikinsu.

Jahar Zamfara, na sawun gaba, wajen marassa ilimin Boko a duk fadin Najeriya. Wanda wannan baya rasa nasaba Da tsofaffin shugabannin da su ka mulki jahar. Misali gwamnan jahar Zamfara na farar hulla na farko a Senator Ahmad Sani Yariman Bakura, ya taimaka matuka gaya a lokacin da yana mulki domin ya assasa makarantannin firamare, sikandire da kuma na gaba da sikandire cikinsu har da kwalejin horar da Malamai da na ci gajiyarsa a shekarun baya. Wanda Kafin shi, makarantar sikandire cewa!

Haka zalika gwamnan ya yi kokarin tallafawa dalibbai a lokacinsa, har a kasashen ketare, Wanda yanzu haka ana cigaba da cin gajiyar ilimin wadanda ya tura din. Duk da shi kansa ba a rasa wasu kura-kurai Da ya tabka musamman bayan ya sauka mulki da ya cigaba da dora wadanda su ka gaje shi kan turba marar bullewa wannan kenan!

Mai daraja tsohon gwamnan jahar Zamfara Mamuda Aliyu Shinkafi da ya hau ya yi iya yinsa, sai dai maganar gaskiya daga gare shi aka samu mummunar matsalar tabarbarewar sha'anin ilimi.

Daga nan gwamnan Da ya sauka kasa da watanni biyu, Mai daraja tsohon gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Abdul'azizu Abubakar Yari ya hau, bayan ya hau ya yi kokarin gyara wasu daga cikin makarantannin firamare da sikandire. Daga cikinsu akwai makarantar Dan Turai sikandire Da firamare duk an sauya masu fasali kwata-kwata, sikandire din Dan Turai ko Wasu makarantannin gaba da sikandire ba su Kai su ba. Haka abun ya ke a makarantar firamare ta JNI, itama a Gusau da sauransu a lungu da sako na jahar Zamfara.

Sai dai kash! Mummunan ta'adin da gwamnan ya yi wa bangaren ilimi wallahi ba ni tunanen nan da Shekaru ashirin za a iya gyara shi.

Domin na farko dai ba a taba samun gwamnan Da bai karfafi matasa su yi karatu ba kamar shi, ba. Domin misali ni nan Kai na har na yi Shekaru hudu a kwalejin horar da Malamai da ke Maru, ba a taba ko Da Tantance ni ba, balantana in samu damar a tallafa Mani, har yau Gani kusa da Kammala jami'a. Hakan ya sa da dama daga cikin takwarorina sun lalace ba ilimi, Domin ba Mai tallafa masu.

Yanzu haka akwai Jarabawar Neco ta 'ya'yan talakawa ta 2018 ba a sako ta ba, maganar NEBTEB ba ta taso ba. Domin Shekaru uku kenan Jarabawar dalibbai da ke sikandiren kere-kere ba a sako masu ita ba.

Har gwamnan ya Shekara takwas bai dauki Malami daya aiki ba, duk kullum suna barin sashen karantarwar Saboda rashin biyansu albashi Mai tsoka, Domin har yanzu akwai Malami a Zamfara da bai karbar naira dubu goma a Wata, a matsayin albashin karshen Wata. Wasu da dama sun yi ritaya wasu kuma sun yi wafati a makarantar Da na yi sikandire kurrum na San lokacin Gwamnatin Shehi Malami uku ya mutu, har yanzu ba a Maye gurbinsu ba.

Akwai shiraruwa Da kungiyoyin duniya su ke bullowa da su Domin tallafawa bangaren ilimi, Amma kwata-kwata jahar Zamfara ba su da matsugunni, ba zan manta lokacin da ina kwaleji ba. Akwai wani shiri Mai suna Teachers Development Program (TDP) aka bullo da shi domin tallafawa Malamai da dalibbai masu karatun bangaren koyarwa, Da zummar bullo sabbin tsare-tsaren koyarwa ta yadda Yara za su fahinta Da sauri, ina daga cikin dalibbai masu hazakar da aka dauka, the tare da bamu horo, da zummar za a tallafa muna in mun Kammala, Amma alhamdulillahi mun samu horo na musamman na koyarwa, sai dai ga banza, Domin mun samu mun Kammala shirin ba tallafin Saboda Gwamnatin ba ta bada na ta kaso ba, haka mu da mu ka samu horon ba a ba Kalle mu ba, Dan kar a yi nasarar ilimin. Hasalima da dama daga cikinmu, na nan suna zaman kawai, ba tare da sun samu inda za su koyar ba. Da Sauran matsaloli da dama!

Ba manta ba, akwai lokacin da aka yi maganar jami'a tsohon gwamna Yari Da bakinsa ya ce, yanzu jahar Zamfara ba ta bukatar jami'a Domin ko kasonta a makwatan jahohi ba ta iya cike wa, Dan haka ba a daukar kudin al'ummar jahar a gina jami'a wasu su amfana Da ita. A lokacin mun yi ta kunfar baki da tada jijiyoyin wuya da wannan kalaman nasa. Domin bayan wasu jajirtattu sun dage damtse an kawo jami'ar, mun tabbatar da da cewa lalle maganar tsohon gwamnan gaskiya ce. Domin yanzu haka in za ka shiga jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, ka tarar Kashi saba'in zuwa tamanin na masu karatu cikinta baki ne, daga jahohin da sunayensu ma wahalar fada ya ke yi muna. Sai dai abunda ya daure muna Kai shi ne, yadda tsohon gwamnan ya sama jami'ar Ido, ba tare da ya tallafa Mata da ko Da daki daya ba, kamar yadda sauran takwarorinta gwamnonin jahohin ke kokarin sun tallafawa jami'o'in da aka kawo masu Dan Amfanin kansu. Hakan ya sa yanzu ko da kana Dan jahar Zamfara kana Da dukkanin takardun da sunka cancanci a dauke ka, ba ka Da tabbacin za a dauke ka. Kuma duk wannan bai rasa nasaba da yadda Gwamnatin jahar ta zura Mata idanu ba tare da ta tallafa Mata, Domin yin ba-ni-gishi-in-baka-manja ba.

Kwatsam! Sai mu ka ji labarin wannan gwamnan shi ne, Da ya kasa tallafawa jami'ar da aka kawo kasa kyauta, kuma ya kasa tallafawa bangaren ilimin kamar yadda ya dace. Shi ne zai fito ya ce zai yi jami'a a garinsu.

Wanda tuni ya bayar da fili har an Fara aiki.

Sai dai abun mamaki, mafi yawan jami'o'in kasarmu, Sukan Fara, daukar Malamai tare da samu wuri da za a Fara karatu na wucin gadi, tare da farawa da karatun share fagen shiga jami'a. Amma shi Rana daya ya dauko wasu Manyan kwasa-kwasassai da da sai jami'a ta bunkasa ake samun damar yinsu. Haka zalika jami'ar har yanzu ba a dauki ko Shugabanta, da registrar ba. Uwa uba sauran Malamai kuma a ce wai har an baiwa dalibbai gurbin karatu!

Anya jami'a wasa ce?

Anya ba manufar gurgunta jahar Zamfara, aka bullo da shirin jami'ar a daidai lokacin da ya zama kasa da watanni ya sauka mulki ya kafata ba.

Abun tambayar ma,

Shin Gwamnatin jahar Zamfara ta na da karfin tattalin arzikin cigaba da gudanar da jami'ar?

Su wane ne za su zama malaman jami'ar, Anya a Zamfara akwai su?

Shin dalibban da za su samu gurbin karatu, Anya Zamfarawa za su fi rinjaye?

Shin daga 2011 da ya hau mulki har ya bayyana Zamfara ba ta da halin Gina jami'a zuwa karshen 2018 da aka ce za a bude jami'ar.

Wane tallafi Gwamnatinsa ta baiwa bangaren ilimi wanda ya sauya halin da ake cikin na rashin masu neman gurabun karatun?

Wace hanyar samun kudin gwamnatinsa ta bude Domin samarwa jahar Zamfara, hanyoyin kudin shiga da za ta iya rike jami'ar?

Shin da a tallafawa sha'anin ilimi ta hanyar daukar malaman firamare, sikandire, da malaman gaba da sikandire da ake Da matukar karancinsa, da inganta walwalarsu, da Kara masu albashi, dama tallafawa dalibbai ta hanyar biya masu kudaden makarantar gaba da sikandire, tallafa masu da yan kudade lokaci-lokaci, tallafawa wasu su yi karatu a wasu kwasa-kwasassai a kasashen duniya tare da Biyan kudaden Jarabawowin dalibban na Waec, Neco da NEBTEB wane ya fi alfanu?

Shin a yi amfani da dukiyarmu wajen gina mu shi ne mafi alheri gare mu ko Gina wasu?

Shawarata ita ce, ina baiwa Mai girma gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Mohammed matawallen Maradun. Shawarar ya dubi shawarar da aminsa su ka ba shi, ta hanyar binciken kwakwab tare gano duk Wata almundahana da aka yi na gina jami'ar. Abunda aka karbo sai ya cika gurinsa na tallafawa matasa su samu ilimi tare inganta sha'anin ilimin zuwa gaba, idan jahar Zamfara ta dawo kan gajiyarta, sai a cigaba da ginin jami'ar.

Haka zalika ina baiwa Mai girma gwamna shawara Da ya dubi yuyuwar hada guiwa da jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Gusau, Domin sanya kason jahar Zamfara wajen Gina jami'ar tare da sharadin fifita dalibban jahar wajen bayar da gurbin karatu fiye Da sauran jahohin Najeriya kamar yadda takwarorinta su ke. Wanda muddun aka yi haka nan ba da Dade ba, jahar Zamfara za samu al'ummar masu ilimi tare da gina Jami'o'i ba ma daya ba Mallakar jahar.

Allah ya sa mu dace ya sa wannan kwarya-kwaryar wasika tawa ta Kai ga kunnuwan wadanda na yi ta Domin su. Allah ya daukaki jahar Zamfara, Da 'ya'yanta ya kawo muna zaman lafiya Mai dorewa.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

11-7-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here