GWAMNATIN JAHAR TA YI TATTAUNAWA TA MUSAMMAN DA SARAKUNAN NOMA, FAWA, ZANGO DA SARAKUNAN SAMARI. AKAN MATSALAR TSARON JAHAR. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 13 July 2019

GWAMNATIN JAHAR TA YI TATTAUNAWA TA MUSAMMAN DA SARAKUNAN NOMA, FAWA, ZANGO DA SARAKUNAN SAMARI. AKAN MATSALAR TSARON JAHAR.





A cigaba da yunkurin Gwamnatin jahar Zamfara. Ta ganin ta shawo kan matsalar tsaron da jahar ke fuskanta.

Taron dai Wanda ya gudana ne a fadar Gwamnatin jahar da ke Gusau.

Taron Wanda ya hada da Sarakunan Noma, fawa, samari da Sarakunan Zango na jahar Zamfara.

Kacokan dai wannan zaman an shirya shi ne, domin samun hadin kan wadannan Sarakunan domin samun Zaman lafiya, jahar Zamfara.

A cewa sarkin Zamfaran Anka Wanda shi ne ya wakilci sauran sarakunan kananan 17 na jahar Zamfara.

Wanda ya bayyana cewa: " Kamar dai yadda kuka gani tun da wannan Gwamnatin ta kafu Mai girma gwamna ya gayyato Yan banga, yan sa-kai da Sarakunan Fulani. Domin tattaunawa da su akan yadda za a samu zaman Lafiya a jahar Zamfara. Wanda alhamdulillahi an samu saukin matsalar matuka gaya a halin yanzu, Domin dukkanin bangarorin sun dauki aniyar bayar da taso gudunmawa Domin kawo karshen matsalar.

Yanzu kuma ga shi mun gayyato ku Domin Ku ne ku ke da kashi saba'in cikin dari na Al'ummarmu. Shi ya sa mu ka gayyato ku, musamman domin tattaunawa da neman hadin kanku domin Samar da tsaro a jahar nan. Kuna da matukar muhimmanci a cikin Al'ummarmu.

Dukkanin bangarorin hudu na shuwagabannin sarakunan da su ka yi jawabi a Madadin wadanda su ke jagoranta, sun nuna jin dadinsu matuka gaya, ga kamun luddayin wannan Gwamnatin, inda sun ka yi alkawarin bayar da gudunmawarmu dari-bisa-dari Domin kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar jahar Zamfara. Wanda ko ba komi dai su ne matsalar ta fi shafuwa.

Taron dai ya samu halartar Mai daraja Mataimakin gwamnan jahar Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Gusau, Mai Martaba Sarkin Zamfaran Anka, ALH. Attahiru Muhammad Ahmad, Sakataren gwamnatin jahar Zamfara Hon. Bala Bello Maru, Sarkin Noman Zamfara Alh. Hassan Muhammad kwazo Gusau, Sarkin Sarkin Fawa, Alh. Sarkin Fawa Malami, Da dukkanin Sarakunan bangarorin na jahar Zamfara.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
13-7-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here