Assalamu Alaikum bayan sallama irin ta addinin da mu ka yi tarayya da kai, ina da fatan kana cikin ƙoshin lafiya, haƙiƙa ina da yaƙinin wannan wasiƙa tawa za ta riske ka.
Ko shakka babu mai girma tsohon gwamnan jahar Zamfara, mun yi mamaki matuƙa da mu ka ji ka fito ranar 20-7-2019 a Gidan rediyon BBC HAUSA kana ɓaɓatu akan cigaban da ake samu kan matsalar tsaron jahar Zamfara. Abun mamaki har da faɗin wai bai dace gwamnati ta yi sulhu Da masu tada Zaune tsayen ba.
Shakka babu mun kaɗu matuƙa gaya, da ma mu ka ji ka iya buɗa baki ka ce kanzil akan matsalar tsaron da za mu iya bugun kirji mu ce kai ne ka haifar da ita. Hujja a nan ita ce; Kafin zuwan Gwamnatinka tabbas akwai matsalar tsaro a Zamfara. Sai dai a lokacin matsalar ba ta taka Kara ta karya ba. Domin kwata-kwata ba za ka ji an kashe gomman mutane a zamfara ba. Amma a lokacin mulkin Gwamnatinka ne. Mu ka san an fara kashe sama da mutum dari biyu a rana ɗaya tilo, Wanda al'ummar Kizara ka ƙaramar hukumar Tsafe, 'Yar Galadima a ƙaramar hukumar mulkin Maru na ɗaya daga cikin wuraren da aka fara samun masifar kisan kiyashi a Zamfara. Sannu-sannu abun ya mamaye duk Zamfara baki ɗaya, wanda sai da aka wayi gari duk Zamfara babu ƙaramar hukumar da ke Zaune lafiya.
Wanda halin ko-in-kula da rashin maida hankali da Gwamnatinka ta yi, ya sa alamurran tsaron jahar suka yi mummunar taɓarɓarewar da Zamfara ta zarce kowace jaha wajen zubar da jinin bayin Allah wanda duniya kaf! Ta shedi haka. Domin har sai da aka wayi gari har a ƙasashen Turai an fara yin zanga-zanga dan nemawa mu Zamfara ɗauki.
Amma Kiri-kiri a lokacin mulkinka ka zura Ido ana ta kisan al'umma ba dare ba rana, sai yawace-yawacen banza a ƙasashen ƙetare. Tare yin kunnen uwar shegu da al'umnarka. Hasalima matakan da kai ka yi ta ɗauka da muƙarabanka a lokacin sun ƙara jefa jahar Zamfara cikin masifar da ka barta ciki.
Domin idan mu ka dubi matakin da Gwamnatinka ta ɗauka na hana sayar Da shanu a mafi yawan kasuwannin jahar Zamfara. Wannan ya jefa Fulani da suka dogara da kiyon shanu, in lalura ta Kama su, su sayar da ɗaya ko biyu su yi lalurarsu, Dan haka hanin ya jefa su cikin Mummunan hali, Wanda hakan ya sa da dama daga cikin fulanin su ka ɗauki ɗabi'ar garkuwa da mutane, domin karɓar kuɗin fansa.
Haka idan mu ka dubi matakin da ka ɗauka na ɗaukar 'yan sa-kai 500 a kowace ƙaramar hukumar mulki a Zamfara. Wannan matakin ya taimaka matuƙa gaya wajen ruruta wutar rikicin dama haɓɓaka wannan matsalar. Domin matsalar tsaron Zamfara ba matsala ba ce buƙatar fito-na-fito ba. Amma Saboda wannan matakin sai aka ja daga tsakanin 'yan sa-kai ɗin da Fulani makiyaya.
Haka zalika idan mu ka dubi matakin da Gwamnatinka ta ɗauka na takaita yawo Da babura a cikin Manyan garuruwan jahar Zamfara, ya taimaka matuƙa gaya wajen jefa talakawan jahar Zamfara cikin ƙunci da ya Haifar da masifu kala-kala da ma ƙarin rashin ayukkan yi musamman ga mu matasa, Wanda ya taimaka wajen ingiza wasu matasa wajen harkar ta'adanci, a zamfara.
Idan mu ka dubi matakin da ka ɗauka na hannunta ragamar tsaro ga hannun tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi da lamurran Masarautu Ɗankande Gamji, wanda ya yi amfani da damar da yake da ita wajen ƙara rura wutar rikicin. Domin kai tsaye wannan kwamishinan ya rinƙa furta kalaman ƙiyayya ta'addanci da tada Zaune tsaye zuwa ga fulani. Wanda a lokacin kai tsaye wannan kwamishinan ya ce duk inda aka ga Bafullatana a kama ta, da sauran kalamai da su ka ƙara munana wannan rikici.
Kwatsam cikin iyawar Allah, ya kawar muna da Gwamnatinka, tare da maye muna ita da gwamnati mai ci a yanzu. Wanda alhamdulillahi duk wanda ya ga kamun luddayi da matakin da wannan gwamnan ya fara ɗauka na sulhu da waɗannan bayin Allah da tashi tsayen da ya yi akan wannan matsalar, dole ya yabawa wannan ɗan tahaliki musamman ganin sauƙin matsalar da aka fara samu.
Wanda a tunanenmu da kana kishin jahar jahar da rayukkan da ake rasawa da dukiyoyin da kai ne mutum na farko da za ka fara fitowa ka yaba wannan Gwamnatin, sai dai kash! Akasin hakan ne ya fito daga bakinka, wanda a madadin yabo domin ƙarfafawa matakin da ya fara ɗora jahar kan turbar zaman lafiya, sai kushe wa matakin ka yi.
To sai dai mai girma tsohon gwamnanmu zan so ka amsa Mani wannan tambayoyi;
Cikin ƙasa da watanni biyu
Gwamnatin da ke ci yanzu a jahar Zamfara sanadiyar sulhun da ta ke cigaba da yi, kisan kiyashi ya ragu matuƙa gaya, garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, da satar shanu su ma duk sun ragu matuƙa gaya. Haka zalika Fulani 'yan asalin jahar Zamfara da gwamnatinka ta haramtawa zama jahar da hulda da al'umma yanzu sun Fara samun 'yancinsu domin gwamnati ta ba su damar shiga kasuwa su sayi abunda su ke so, abunda Gwamnatin ta hana baya. A cikin waɗannan kwanakin na wannan gwamnatin zuwa yau da na ke wannan rubutun an yi nasarar karɓo mutum 147 a hannun 'yan bindiga ba tare da zubar da jini ko biyan diya ba, yayin karɓo su. Tashin hankali da tsoro ya ragu matuƙa gaya, a cikin zukatan Zamfarawa. Haba mai girma tsohon gwamnanmu. Duk wannan bai dace a yaba ba, sai dai kushewa.
Mai girma tsohon gwamna, tambaya ta nan, ita ce;
Ka shekara 8 kan karagar mulkin jahar Zamfara, mun ga dukkanin take-taken Gwamnatinka, da yadda ka yi tu'ammali da matsalar tsaron. Wanda mu dai kai ne mu ka fi zargi wajen ruruta wutar rikicin.
Tunda da ka ce kar a yi sulhu, yanzu!
Me ya sa matakan da ka bi su ka ki tasiri a baya?
Me kake son wannan gwamnatin ta yi?
Me ya hana ka yi amfani da abunda ya dace, lokacin da kana kan karagar mulki?
Shin fulanin da ka ce kar a yi sulhu Da su, me za a yi masu, Anya za ka ji daɗi a cigaba da zubar da jini a Zamfara?
Ya mai girma tsohon gwamnanmu, mu dai da so na zama samu da ka kame bakinka, ta hanyar dena tsoma baki ga wannan Gwamnatin, domin ka yi naka lokaci mun gani, kuma muna rokon Allah ka da ya ƙara maimaita muna gwamnati irin taka, domin mu dai wallahi kwata-kwata muryarka ko wani Abu da ma ya shafe ka, wallahi ba mu son ji, domin wallahi mun dai gaji.
Daga ƙarshe muna baiwa mai girma gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Mohammed matawallen Maradun shawarar da kwata-kwata kadda ya dubi wannan ruɓaɓɓiyar shawarar tsohon gwamnan ta wai dena sulhu da waɗannan 'yan bindigar. Kasancewar mu dai da ke cikin jahar muna ganin alfanun sulhun, kuma muna Da yaƙinin zai ci gaba da tasiri kamar yadda mu ga ya fara. Hasalima muna zargin cewa tsohon gwamnan ya fara waɗannan maganganu ne domin nasarar da ya ke ganin wannan gwamnatin na samu ta fuskar tsaro wanda nasarar na nufin kawo ƙarshen duk wani tasiri nasa a siyasar jahar zamfara musamman a 2023 da ya ke iƙƙirarin zai ɗora yaransa.
Da haka mu ke roƙon Allah ya riƙawa wannan Gwamnatin ya ƙarfafe ta wajen yiwa al'ummar jahar Zamfara abun kirki. Allah duk wani sharri da masifo da ke tattare da wannan sulhu, Allah ka kawar muna da shi, Allah duk waɗanda ba su son wannan sulhu ya ɗore dan biyan bukatunsu, Allah ka da ka cika masu gurinsu.
Allah muna roƙonka ka kawo muna zaman lafiya Mai ɗorewa a jahar Zamfara da Najeriya baki ɗaya.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

