Tun dai bayan da kotun ƙoli ta yanke hukucin cewa jam'iyar APC a jahar Zamfara ba ta gudanar Zaɓen fitar da gwani na jam'iyar a jahar ba, Wanda ya baiwa jam'iyar PDP damar kafa Gwamnatin da Bello Muhammad Matawallen Maradun ke jagoranta a matsayin gwamna daga jam'iyar PDP, wanda ya yi ƙawance da ɓangaren APC din da su ka kira kansu G8 waɗanda suka ƙalubalanci yuƙurin Abdulazeez Abubakar Yari har su ka yi nasara akansa.
Dukkanin ɓangarorin ke haƙorrin cewa tabbas bangarensa ne, za a baiwa minista Daga zamfara
Sai dai kwatsam ranar 23-7-2019 sunayen waɗanda shugaban ƙasa ya zaɓa a matsayin waɗanda su zai naɗa a matsayin ministoci ya bayyana. Sai dai kwatsam! aka ga sunan Sadiya Umar Faruk, wadda ba a taɓa tsammanin za a ga sunanta daga jahar Zamfara ba. Domin magoya bayan APC ɓangaren YARI na hasashen shi ogan nasu za a baiwa. Haka zalika ɓangaren G8 na hasashen ɗaya daga cikin 'yan G8 din ne za a baiwa. Sai dai kwatsam ga sunan ita sadiyar wadda Kwamishiniyar kula da 'yan gudun hijira ce ta Gwamnatin Tarayya.
Sai dai bayan Fitar da sunanta din da dama daga cikin 'yan 8G ba su ji daɗi ba domin a tunanensu Shi ne ɗaya ga cikin jagororinsu ne za a baiwa, ministan. Sai dai da su ka tuna da cewa ai ita din ma ɓangarensu take, har tana daga cikin mutanen da Shugaban jam'iyar APC ɓangaren Yari ya kora daga jam'iyar da wasu jiga-jigan G8 a cewarsa suna yiwa jam'iyar bita da ƙulli. Sai su ka cika da murnar yin galaba, kan Yari. Wannan kenan.
Wanda shi kansa ɓangaren yarin an ruwaito da dama na aibata shugaba Buhari a Soshiyal Midiya na rashin zaɓen ogan nasu.
Sai dai kwatsam mu ga tsohon gwamnan na Zamfara tare da ita wadda za a naɗa ministar. Abunda ya baƙanta ran 'yan G8 sai dai mun jiyo wasu na cewa duk shure-shure ne na tsohon gwamnan Wanda bai hana shi mutuwa, domin haka ya yi ta yiwa shugaba Buhari kafin zaɓe Dan neman ya ɗaure masa gindi a ya yi zaɓinsa a Zamfara, amma bai yi nasara ba. Haka kuma abun ya kasance bayan yana neman minista kullum yana ƙugun Tenubu, Osinbanjo da sauran jiga-jigan APC Amma Hakan bai tsinana masa komi ba.
Ba zato ba tsammani, sai mu ka jiyo muryar tsohon Kakakin jam'iyar APC na jahar Zamfara kuma Mataimakin shugaban jam'iyar a yanzu na Zamfara ta Tsakiya wato Sani Gwamna Mayanci, Wanda ɗan gani kashenin Yari din ne ya fito, yana ɓaɓatu a kafar yaɗa Labarai ta gidan Rediyon Jamani cewa shugaba Buhari bai yi masu adalci ba, domin Sadiya Umar Faruk ba ta cikin sunayen waɗanda su ka Turawa shugaban a matsayin a yi mata minista, asali Suna Allah waddai da zaɓinta.
Bai rufe bakinsa ba, sai mu ka jiyo, Kakakin jam'iyar APC na Zamfara duk dai a ɓangaren Yarin wato Shehu Isah Gusau a wani bidiyo da su ka watso yanar gizo, yana Allah waddai da kalaman sani gwamna tare kare kansu da maganar, da Wanda ya gada ya furta. Inda ya bayyana cewa ɓangaren Yari na maraba da Zaben Sadiyar. Kuma ba su tare da kalaman Mataimakin shugaban jam'iyar
Ko dai mene ne lokaci zai nuna! Shin tsakanin Mataimakin shugaban jam'iyar da ya bayyana ba su tare da shugaban da shi kuma Kakakin da ya bayyana cewa dari-bisa-dari suna tare da shi. Wa ya yi magana da yawon jam'iyar.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
27-7-2019

