MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA TA YABA DA KAMUN LUDDAYIN DAN MAJALISSA MAI WAKILTAR GUSAU DA TSAFE. TARE DA ROKONSA YA CIGABA.... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 31 July 2019

MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA TA YABA DA KAMUN LUDDAYIN DAN MAJALISSA MAI WAKILTAR GUSAU DA TSAFE. TARE DA ROKONSA YA CIGABA....




A jiya Talata 30-7-2019 kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen jahar ta kaiwa, Dan Majalissar Tarayya Mai wakiltar Gusau da Tsafe Hon. Kabiru Amadu Maiplace ziyarar taya ta farko tun bayan samun nasararsa na zama Dan Majalissar Tarayya. Ziyarar dai kacokan 'ya'yan kungiyar ta Muryar Talaka sun Kaita nemin Mika sakon talakawan jahar Zamfara. Tare taya Dan Majalissar murnar zama Dan Majalissar da kuma jinjina masa akan salon kamun luddayin jagorancinsa na tallafawa masu Dan karamin karfi domin ingantar da rayuwarsu.

A jawabin shugaban kungiyar ya nuna muhimman ayyukan da Hon *Kabiru Amadu* mai palace da ya dauko ga Al'ummar da ya ke wakilta su ne manufar aikin Muryar Talaka kamar yadda Al'ummar jiha suka sani,

Kungiyar ta jinjina masa akan haka, Dan haka za ta yi tafiya kafada-da-kafada da ayyukan da ya sanya a gaba, domin dukkan 'ya'yan Muryar Talaka sun aminta da ya zama daya daga cikin Ginshidan kungiyar Muryar Talaka a fadin jiha baki daya 

Ya kara yaba masa yadda yake kokarin bayar da tallafin karatu ga Matasanmu, da kuma bayar da tallafin sana'o'in ga uwayenmu mata. Da kuma tallafawa Matasan da su ka wahala da shi a lokacin yakin neman zabe Wanda wannan abun farin ciki ne.

Da yake maida jawabi Hon *Kabiru Amadu* ya yi Matukkar farin ciki da murna game da wannan ziyarar, ya kuma jinjinawa kungiyar akan yadda, duk shekara kungiyar take kawo ayyukan cigaba a cikin Al'ummar jiha baki daya.

Ya tabbatarwa kungiyar dukkan shirarukan da ya kawo na cigaba a cikin al'umma zai sanya Muryar Talaka a ciki, ya kara da cewa yanzu haka ga wani aikin cigaban Alumma da ya kawo ya ke son Murayar Talaka ta aiwatarwa da shi.


Daga karshe Dan Majalissar ya yi alkawarin tallafawa shirin da kungiyar muryar talaka ta dauko na tallafawa, yara Marar Galihu musamman Almajirai. Inda ya baiwa wannan kungiyar aikin cigaba na ta shiga cikin fadin Gusau da Tsafe domin aikin kididdige makarantunmu na addini, domin sanin ta hanyar da Ya kamata a taimaka mu su, daga nan ya karfafe mu da mu tashi tsaye domin yin aikin ba dare ba rana wajan taimakawa Al'umma.



Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta kasar Reshen Jahar Zamfara) 

31-7-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here