A Cigaba sulhun da Gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Mai girma gwamna Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ke yi. Domin Samar da tsaro a jahar Zamfara. A yau kwamitin farfado da zaman lafiya a jahar Zamfara Da Gwamnatin jahar Zamfara ta kafa, karkashin jagorancin Tsohon Sufeto Janar na 'yan sandar Najeriya. Ya yi Wa manema Labarai Jawabi akan nasarorin da kwamitin su ya ke cigaba da samu wajen kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara.
Ciki har da sako wani mutum Dan kasar Korea da ya yi Watanni Bakwai a hannun masu garkuwa da mutane. Da wani Dan Najeriya da aka yi garkuwa da su tare.
Shi dai wannan Bature da ba a aminta manema Labarai su bayyana sunansa ba, ma'aikaci ne, a Assibitin Tsafe. 'yan bindiga sun yi garkuwa da shi a karamar hukumar Tsafe, watanni Bakwai baya tare da wani bawan Allah da ke yi masa hidima Wanda shi kansa Dan karamar hukumar tsafe ne.
Kwamitin ya bayyana matukar godiyarsa ga al'ummar jahar Zamfara na goyon baya da addu'a ake yiwa kwamitin.
Haka zalika ya bayyana matukar jin dadinsu da yadda 'yan bindigar su ka yarda za su Mika wuya, tare da bayar da gudunmawa wajen kawo karshen matsalar tsaron a jahar Zamfara. Wanda zuwa yanzu a Cewar tsohon Sufeto Janar din an yi nasarar sakin mutum 250 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a baya. Haka zalika kwamitin ya nuna matukar godiyarsa da yadda Gwamnatin jahar Zamfara ke baiwa kwamitin su goyon baya dari-bisa-dari.
Zaman kwamitin dai ya samu hakartar Shi kansa shugaban kwamitin MD Abubakar Gusau, Senator Saidu Dansadau, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, Hon. Abubakar Justice Dauran da sauran Muhimman jama'a.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.



