Majalisar dokokin jahar Zamfara ta aminta da dakatar da shugaban karamar hukumar mulkin Maradun, da kuma uban kasar Boko ta yamma, bisa zarginsu da hannu wajen yiwa shirin samar da zaman lafiya na gwamnatin jaha zagon kasa. Haka zalika majalisar ta aminta da sauya matsayin masarautar bazai zuwa matsayinta na fari. wato uban kasar bazai, da kuma uban kasar Talatar Mafara. kamar yanda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito.
Mahmud Salihu Kaura Namoda

