'YA'YAN JAM'IYAR APC SAMA DA DUBU 20 SUKA SAUYA SHEKA ZUWA PDP A ZAMFARA CIKI HAR DA TSOHON MATAIMAKIN GWAMNA, TSOFAFFIN SHUWAGABANNIN MAJALISSAR DOKOKI, TSOFAFFIN KWAMISHINONI... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 8 August 2019

'YA'YAN JAM'IYAR APC SAMA DA DUBU 20 SUKA SAUYA SHEKA ZUWA PDP A ZAMFARA CIKI HAR DA TSOHON MATAIMAKIN GWAMNA, TSOFAFFIN SHUWAGABANNIN MAJALISSAR DOKOKI, TSOFAFFIN KWAMISHINONI...

S







ama da mutum dubu ashirin ne magoya bayan jam'iyar APC a jahar Zamfara su ka sauya sheka zuwa jam'iyar PDP a yau. Ciki har da tsohon Mataimakin gwamna, Muktar Ahmad Anka, tsofaffin shuwagabannin Majalissar dokokin Zamfara Hon Muhammad Bawa Gusau da Hon Abdullahi Bature Umar Sambo, tare da tsohon Mataimakin shugaban Majalissar dokokin Zamfara Hon Namadi Isa Kasuwar Daji, tare da tsofaffin Kwamishinan Biyar 5 da masu tsofaffin masu baiwa gwamna Shawara, sun sauya sheka zuwa jam'iya Mai ci-a-yanzu a jahar Zamfara. Wato PDP.

Dukkanin wadanda su ka sauya sheka sun bayyana haka a dandamalin bikin karbarsu da ya gudana a gidan Gwamnatin jahar Zamfara da ke Gusau. 

Mai girma gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Mohammed Matawalle  ne ya karbe su. Kuma ya tabbatar masu da cewa Gwamnatinsa za ta dauke su bai daya, ba tare da nuna bambanci tsakanin su da takwarorinsu da su ka isko a PDPn ba. Domin babban gurinsa shi ne ciyar da Zamfara gaba. 

Gwamnan ya yi kira gare su da su tashi tsaye wajen wayar da kan al'umma muhimmancin hada hannun domin cigaban Gwamnatinsa da ke da kudurin ciyar da al'ummar jahar gaba.

Haka zalika gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatinsa za ta cigaba da ayukkan tallafawa rayuwar marassa Galihu ta hanyar girkiro hanyoyin da za su rage radadin rashin da Al'umma su ke fama da shi a jahar Zamfara He maintained that his administration.

A jawabansu daban-daban a wajen bikin wankan In their separate speeches tsohon Mataimakin gwamnan jahar Zamfara , Alhaji Muktar Ahmad Anka, Hon Abdullahi Bature Umar Sambo and Hon Muhammad Bawa Gusau sun bayyana cewa sun yanke shawarar Koma jam'iyar PDP ne, domin yin na'am da su ka yi da kamun luddayin Gwamnatin gwamna Matawalle na samar da zaman lafiya ga al'ummar Zamfara.

Haka zalika sun bayyana cewa,  zaman lafiyar da aka soma samu ya irin manufa da Gwamnatin ta ke da shi na Dora jahar Zamfara akan tafarkin cigaba. Wanda kowane Dan jahar Zamfara zai so ya zama daya daga cikin wadanda ake damawa da su domin kawowa jahar cigaba Mai dorewa. Daga karshe sun bayyana cewa za su tallafawa gwamnan domin samun nasarar gwamnatinsa 

Wadanda su ka yi wankan dai sun hada da:, Alhaji Muktar Ahmad Anka, Tsofaffin shugabannin Majalissar dokokin jahar Zamfara biyu, Hon Muhammad Bawa Gusau da  Hon Abdullahi Bature Umar Sambo da tsohon Mataimakin shugaban Majalissar dokoki Hon Namadi Isah Kasuwa Daji.

Sauran sun hada da: Tsofaffin Kwamishinoni, Hon Abdullahi Mohammed Gurbin Bore,Hon Ango Umar Bakura Hon Kabiru Ahmad Janyau and Hon Engr Mustapha Musa Mayana.

Sai kuma Tsofaffin masu baiwa gwamna Shawara ta musamma,Hon Aliyu Ibrahim Magaji Ajala da Hon Rilwanu Nagambo Anka sai kuma Tsofaffin 'yan Majalissar jahar da suka hada da;  Hon Mannir Aliyu Gidan Jaja da Hon Abdullahi Danyaro Wuya tare da Mataimakin shugaban karamar hukumar Zurmi Mai ci-a-yanzu Hon Mainasara Atiku Zurmi da sauran Tsofaffin masu baiwa gwamna  Shawara da masu magoya bayansu da kungiyoyinsu da kuma iyalansu 

YUSUF IDRIS GUSAU
Babban Daraktan Watsa Labarai A Fadar Gwamnatin Jahar Zamfara 
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau 
08/08/2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here