Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara, Hon. Dr. Belllo Muhammad Matawallen Maradun ya ziyarci babban gidan yarin jahar Zamfara. Inda ya yi wa masu Kananan Laifukka da masu Kananan basukka afuwa.
Da ya ke Jawabi a wa harabar babban gidan yarin na Gusau. Gwamnan ya ja hankalin wadanda aka yiwa afuwar. Da su ji tsohon Allah, su kuma zama jakadu nagari Idan sun Koma a cikin Al'umma.
Haka zalika gwamnan ya ja kunnen wadanda aka yiwa afuwar da su debe kowa a ransu, na cewa shi ne silar zuwansu wannan gidan. A madadin Hakan su daukar matakin ramuwa ga wadanda su ka yi sanadiyar Shigarsu gidan ko matara Kama da haka.
Gwamnan ya baiwa fursunonin gidan buhun shinkafa 100 shanu 5 da kuma raguna 10 domin yin hidimar sallah
Cikin wadanda aka yiwa afuwar maza 140 ne. 5 daga cikinsu wadanda aka yankewa hukucin kisa, 5 wadanda aka yankewa Daurin rai da rai a gidan yarin, mutum 30 wadanda aka daurewa hukuci. Sai mutum 60 da ke zaman Hiram a yanke masu hukunci, sauran mutane 41 Tsofaffi ne, da wadanda su karance Alkur'ani da wadanda ba su da lafiya. yayin da sauran mutum 9 kuma mata ne kuma su ne matan da ke gidan yarin.
Daga nan gwamnan ya zagaya dukkanin dakunan kwanan fursunonin, domin ganin halin da dakunan ke ciki, da assibitin gidan tare da wajen dafuwar abincin fursunonin.
A lokacin da ya ke maida Jawabi shugaban hukumar ma'aikatan gidajen Yari na jahar Zamfara, ya nuna matukar jin dadinsa da ziyarar da gwamnan ya kawo masu, in ya bayyana cewa, gwamnan shi ne gwamnan da yafi mutunta bukatun masu zama gidan yarin cikin jahohi 11 da ya yi aiki da su a baya
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
9-8-2019




