GWAMNATIN ZAMFARA TA SHIRYA GAGARUMIN WASAN SHARU, DOMIN NUNAWA DUNIYA ZAMAN LAFIYA, YA DAWO A JAHAR..... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 13 August 2019

GWAMNATIN ZAMFARA TA SHIRYA GAGARUMIN WASAN SHARU, DOMIN NUNAWA DUNIYA ZAMAN LAFIYA, YA DAWO A JAHAR.....


Ganin zaman lafiya ya na cigaba da samuwa a lungu da saĆ™o na jahar Zamfara. Wanda a watannin baya ba a ga maciji tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa Manoma. Wanda Hakan ya sa gaba ta Mai Ć™arfi ta shiga, aka shiga kisan kiyashi da Ć™oĆ™arin shafe juna a doron Ć™asa. Idan Bafullatani ya shigo gari sai buzunsa. Yayinda shi kuma Bahaushe ya zama nama in ya shiga dawa....

Sai dai alhamdulillahi a zaman wannan gwamnati na watanni biyu da kwana 14 yanzu. Cikin ikon Allah gwamnatin na cigaba da samun nasara a yunkurinta na kakkabe duk wani tashin hankali da ke addabar Zamfara. Wanda Hakan ne ya haifar da shiga hanyoyin sulhu tsakanin ɓangarorin, da ke gaba da junan. Wanda alhamdulillahi duniya kaf! Ta Shedi zaman lafiya ya Fara samuwa a jahar Baki ɗaya....

Dan haka ne Gwamnatin jihar zamfara ta shirya wasan sharu ga Fulani da sauran wasanin Fulani ranar Talata 13/8/19 a dandalin Baje koli kan titin Bye pass Gusau da karfe 12 na rana.

Dalilin wannan BIKIN shi ne nunawa Duniya cewa zaman lafiya ya Fara samuwa a jahar, Wanda a baya ko da kuÉ—i Bafullatani ba zai shigo cikin gari ya Koma lafiya ba ruggarsa lafiya ba. Amma yanzu alhamdulillahi hakan ya zama tarihi. 

Muna rokon Allah ya Kai mu lafiya, ya sa a yi lafiya a kammala lafiya. Ya dawo muna da da dauwammen zaman lafiya a jahar Zamfara da Nigeria Baki daya. Ya taimaki gwamnatin Mai girma gwamna Bello Matwallen Maradun

 Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

13-9-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here