Mai Martaba sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Faruk Umar CON Ya aminta da naɗa gwamnan jahar Zamfara Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun da SARAUTAR Barden Hausa.
A takarar da aka mik
Ƙa wa gwamnan wadda ke ɗauke da sa hannun sarkin Daurar ta nuna cewa Masarautar ta yanke wannan hukucin la'akari da jajircewar matawallen wajen aiki tukuru domin taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a ƙudurinsa na dawo da zaman lafiya a ko'ina cikin Tarayyar Najeriya ne ya sa su ka ga ya cancanci wannan SARAUTAR.
Haka zalika takarar ta bayyana cewa kafin bayar da sarautar sai da su ka tuntuɓi dukkanin Sarakunan ƙasar Hausa 14 wato Hausa Bakwai da na 'yan uwa Bakwai a cewarsa. Waɗanda dukkaninsu sun aminta da naɗa gwamnan zamfarar da wannan SARAUTAR.
Nan gaba dai ne za a yi bikin naɗin wannan sarautar.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
15-8-2019



