A cigaba da kawo maku ayukkan cigaban Al'umma da gwamnan jahar Zamfara Dr. Belllo Muhammad Matawallen Maradun ya ke yiwa al'ummarsa. Insha Allahu daga wannan makon duk jumu'a za mu rika kawo maku bayanai na wasu Muhimman ayukkan alheri da gwamnan ya yi. Asha Karatu lafiya....
1- YIWA FURSUNONI 150 AFUWA!
Ranar 9-8-2019 Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya yi wa fursunoni 1 Cikin waÉ—anda aka yiwa afuwar maza 140 ne. 5 daga cikinsu waÉ—anda aka yankewa hukucin kisa, 5 waÉ—anda aka yankewa É—aurin rai da rai a gidan yarin, mutum 30 waÉ—anda aka É—aurewa hukunci. Sai mutum 60 da ke zaman jiran a yanke masu hukunci, sauran mutane 41 Tsofaffi ne, da waÉ—anda su hardace Alkur'ani da waÉ—anda ba su da lafiya. yayin da sauran mutum 9 kuma mata ne kuma su ne matan da ke gidan yarin.
Gwamnan ya baiwa fursunonin gidan gudunmawar buhun shinkafa 100 shanu 5 da kuma raguna 10 domin yin hidimar sallah
2- YA SHIRYA ƘASAITACCIYAR WALIMA TARE DA MA'AIKATAN FADARSA!
Ranar 11-8-2019 gwamnan ya shirya Walima wadda ta gudana a gidan gwamnan na ƙashin kai da ke GRA Gusau. Wadda ta haɗa da dukkanin jami''an tsaron fadarsa, Direbobi, ma'aikatan kiyon lafiya, 'yan Jaridu da 'yan Social Media na ofishin gwamnan.
A yayin walimar wadda aka ci aka sha nau'unkan abinci kala-kala, gwamnan ya ji Jawabai masu sanyaya zuciya ga duk wani ma'aikacin gidan. Wanda har sai da 'yan sanda su ka waƙe gwamnan da waƙa zazzaka, domin murna.
3- ZUWA AMUSEMENT PARK DA MARAYU DA TARE DA BA SU KYAUTUKKA.
Ranar 11-8-2019 Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Dr Bello Mohammed Matawallen Maradun, ya ɗauki Marayu da ke rayuwa a gidan Marayu da ke Gusau. Inda ya zagaya da su a wajen wasa na Amusement park da ke Gusau. Domin ɗebe masu kewa da rage masu raɗaɗin rashin iyayensu. Daga nan ya ba su kyautukka tare da alƙawarin tallafawa rayuwarsu domin su zama wasu a cikin Al'umma.
4- SHIRYA GAGARUMIN WASAN SHARU, DOMIN NUNAWA DUNIYA ZAMAN LAFIYA, YA DAWO A ZAMFARA
Ranar 13/8/19 Ganin zaman lafiya ya na cigaba da samuwa a lungu da saƙo na jahar Zamfara. Wanda a watannin baya ba a ga maciji tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa Manoma. Wanda Hakan ya sa gaba ta Mai ƙarfi ta shiga, aka shiga kisan kiyashi da ƙoƙarin shafe juna a doron ƙasa. Idan Bafullatani ya shigo gari sai buzunsa. Yayinda shi kuma Bahaushe ya zama nama in ya shiga dawa....
Sai dai alhamdulillahi a zaman wannan gwamnati na watanni Ƙasa da uku yanzu. Cikin ikon Allah gwamnatin na cigaba da samun nasara a yunkurinta na kakkabe duk wani tashin hankali da ke addabar Zamfara. Wanda Hakan ne ya haifar da shiga hanyoyin sulhu tsakanin ɓangarorin, da ke gaba da junan. Wanda alhamdulillahi duniya kaf! Ta Shedi zaman lafiya ya Fara samuwa a jahar Baki ɗaya....
Dan haka ne Gwamnan ya shirya wasan sharu ga Fulani da sauran wasanin Fulani ranar Talata 13/8/19 a dandalin Baje koli kan titin Bye pass Gusau da karfe 12 na rana. Wanda fulani su ka cika su ka batse a wajen domin yin wasanninsu.
5- ZIYARAR BARKA DA SALLAH A MAHAIFARSA
Ranar 14-8-2019 Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara, Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya shiga karamar hukumarsa ta Maradun Inda ya kai ziyarar barka da sallah ga al'ummarsa.
A lokacin ziyarar Gwamnan dai ya gana da Muhimman mutane na karamar hukumar mulkin tasa. Wadanda su ka hada da Uwayen kasar Maradun, kungiyar ma'aikatan Gwamnati ta karamar hukumar Maradun, haka zalika ya gana da kungiyar Tsofaffin ma'aikatan Gwamnati na Maradun, Maradun Progressive Union, shuwagabannin jam'iyar PDP na karamar hukumar Maradun, sai kuma Kungiyar Dalibbai ta Kasa na karamar hukumar Maradun sai kuma 'yan uwa Gwamnan na jini da su ka kawo masa ziyara.
6- ZIYARA ASSIBITI MARADUN INDA YA DUBA MARASSA LAFIYA. TARE DA YIWA MAJINYATA SHA TARA TA ARZIKI...
Ranar 14-8-2019 gwamna, Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya zagaya a Assibitin Maradun, domin duba marassa lafiya. da tallafa masu. haka zalika ya saurari matsalolin da Assibitin ta ke fuskanta Inda nan take ya bayar da umurnin a Gina masu sabuwar Assibiti.
Kadan kenan daga cikin ayukkan gwamnan na wannan makon Insha allahu wani makon za mu kawo maku wasu. Addu'armu a kullum ita ce Allah ya rikawa wannan Gwamnatin ya ba ta cikin yin ayukkan da za su taimaki rayuwar Talaka.
Daga: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
16-8-2019









