GWAMNATIN ZAMFARA TA SAMU LABARIN ZA A KAI HARE-HAREN TA'ADDANCI A CIKIN JAHAR. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 23 September 2019

GWAMNATIN ZAMFARA TA SAMU LABARIN ZA A KAI HARE-HAREN TA'ADDANCI A CIKIN JAHAR.

DAGA FADAR GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA.




Gwamnatin jahar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Hon Dr. Bello Mohammed MON (Matawallen Maradun) tana sanar Al'ummarta cewa, ta samu rahoton cewa wasu daga cikin ɓaragurbin 'yan siyasar jahar Zamfara da ba su ƙaunar cigaban jahar suna yunƙurin tarwatsa jahar.


Waɗannan maciya amanar sun yi hayar 'yan kungiyar Boko Haram domin ƙaddamar da miyagun hare-hare kan al'ummar ba su ji ba su gani ba. Domin tarwatsa zaman lafiyar da al'ummar jahar su ka samu ƙarƙashin jagorancin wannan Gwamnatin.

Kamar yadda Rahoton asirin ya bayyana cewa 'yan ta'addar za su kai miyagun hare-hare a ƙananan hukumomin jahar Zamfara bakwai ciki har da babban birnin jahar Zamfara. Haka zalika Rahoton ya bayyana cewa akwai Muhimman mutane biyu na jahar da za a kashe domin samun nasarar wannan aika-aikar.

Ƙananan hukumomin da za a Kai waɗannan hare-haren su ne: babban birnin jahar Zamfara wato Gusau, wadda za a kaiwa mummunan hari biyu a matsayinta na babban birnin jaha. sai kuma ƙananan hukumomin, Tsafe, Talata Mafara, Anka, Zurmi, Maru da Maradun. Wasu daga cikin wuraren da Rahoton ya ambato cewa za a kaiwa hari a Gusau su ne babban masallacin Juma'a na Gusau da kuma Mammy Market. Domin Suna daga cikin wuraren da aka fi samun cinkoson mutane dare da rana.

Rahoton ya bayyana cewa 'Yan Boko Haram, din da aka yo hayar za su ƙaddamar da hare-haren ta'addancin nasu a tsakanin ranakkun Litinin 23 ga wannan watan na Satumba zuwa 25 ga watan oktober 2019.


Saboda da haka gwamna Matawalle, kamar yadda aka sani ya ɗauki kariyar rayukkan al'ummarsa da dukiyoyinsu da matuƙar muhimmancin gaske. Don haka yana amfani da wannan damar domin kira ga dukkanin al'ummar jahar zamfara musamman na waɗannan ƙananan hukumomin da aka zayyano da su sanya sa ido ga duk wani motsi da ba su yarda da shi ko wata baƙuwar fuska ba, ta hanyar kai rahotonta ga hukuma mafi kusa da su, domin daƙile mummunan shirin da maƙiya jahar su ke ƙoƙarin yi.

Gwamna Matawalle, ya nuna Matuƙar rashin yardarsa  ga wannan mummanar aika-aikar da ɓaragurbin 'yan Siyasa maciya amanar al'ummar jahar su ka ɗauki aniyar ɗaukar rayukka da salwatar da dukiyar al'ummar da ba su ji ba su gani ba, don kurrum su cimma mummunar manufarsu. A cewarsa Sha'anin samar da tsaro, sha'ani ne da ya shafi dukkanin wani ɗan ƙasa nagari, ba tare da bambancin Siyasa ba. Don haka Gwamnatinsa ba za ta zura ido maciya amana su tarwatsa Zamfara ba.



Ƙari akan hakan gwamnan ya yi Kira ga direbobin mota da 'yan Acaba na jahar Zamfara da su Sanya ido matuƙa gaya, a lokacin da su ke gudanar da kasuwancinsu wajen sanar da jami''an tsaro duk Wani Gungun mutane ko wasu kayan da ba su yarda da su ba. 

Gwamnan ya yi Kira ga al'ummar Jahar Zamfara da kada su Tayar da hankalinsu, domin Gwamnatinsa ta ɗauki mataki kwakkwara na jami''an tsaro da za su yi aiki dare da rana suna zagayawa lungu da saƙo na jahar baki ɗaya, domin tabbatar da tsaron rayukka da dukiyoyin al'ummar Zamfara. Ya kuma ja hankalin al'ummar Zamfara da kada su tayar da hankalinsu dan sun ga jami'an tsaro da Manyan Makamai a cikinsu. An shirya haka ne domin tabbatar da tsaron rayukka da dukiyoyin al'ummar.

Gwamnan ya ƙara da cewa; kullum gwamnatinsa cikin aiki take tuƙuru domin tabbatar da ta haɗa Kai da jami''an tsaro, domin Samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jahar.

Haka zalika gwamnan ya nuna matuƙar yabawa ga irin haɗin kai da tubabbun 'yan bindiga da Yan-sa-kai su ke ba shi, na rungumar sulhu Wanda shi ne ya haifar da zaman lafiyar da al'ummar Zamfara ke kwankwaɗar romonsa. Dan haka ya roƙe su da su cigaba dama ƙara ba shi haɗin kan da su ka saba, domin cigaban zaman lafiya a zamfara 

Haka zalika gwamnan ya nuna matuƙar godiyarsa ga tubabbun 'yan bindigar da su ka sako Ƙarin mutane talatin da su ka yi garkuwa da su 15 maza 15 mata da su ka fito daga ƙaramar hukumar Ƙaurar Namoda wanda wasunsu sun shafe sama da watanni takwas a hannun masu garkuwar.

Daga ƙarshe gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun ya roƙi al'ummar jahar Zamfara da su cigaba da goya mashi baya, kamar yadda suka saba. Musamman addu'o'in da su ke yi a cikin salloli biyar kullum a ciki da wajen jahar domin samun zaman lafiya a lungu da saƙo na jahar Zamfara.

YUSUF IDRIS GUSAU 
Babban Daraktan Watsa Labarai a fadar Gwamnatin jahar Zamfara.
22nd September, 2019.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here