Magoya bayan tsohowar Gwamnatin Shehi, sun yada bidiyon wata Makaranta da aka dauko bidiyon yara suna Karatu a cikin aji ruwan sama na zuba.
Inda su ka kira makarantar da Government Day Secondary School Millennium, da ke Gusau. Har su ka dauki laifin halin da makarantar take ciki su ka dorawa Gwamnatin jahar Zamfara mai ci a yanzu. Karkashin jagorancin. Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun.
Alhamdulillahi, saboda dalillai uku tun online mun tabbatar da wannan Makarantar ba GDSS Millennium ba ce. Na farko dai:
1. Duk Zamfara ba makarantar Gwamnati da dalibbai ko na Primary ke Sanya Gajeren Wando.
2- Makarantar da su ka kira GDSS Millennium. Maza da mata ce, ita kuma Millennium Maza ce Zalla.
3 Tsarin ginin makarantar ba irin na makarantun Zamfara ba ne.
Haka zalika mun zagaya cikin a makarantar GDSS Millennium din Inda mu ka ga halin da take ciki tare da zantawa da shugaban Makarantar da Malami da kuma wani dalibi da ke aji Shida.
Inda su ka tabbatar muna da cewa tabbas wannan bidiyon da magoya bayan tsohowar Gwamnati suka yada domin bata sunan wannan Gwamnatin. Karya ne, ba makarantar su ba ce. Sai dai su kansu makarantarsu na cikin wani mawuyanci Hali.
Wanda kamar yadda shugaban makarantar da sauran Malaman makarantar da mu ka zanta da su sun tabbatar da cewa makarantar na cikin mummunan Hali sama da shekaru hudu. Domin ko shugaban makarantar shekararsa uku a makarantar. Amma ko da ya zo ya tarar da makarantar cikin mummunan Hali kuma ya rubutawa Gwamnati matsalar ya fi curin masaki Amma, ko kwaskwarima ba a taba zuwa aka yiwa makarantar ba.
In dai ba a manta ba yau da na ke wannan rubutun watannin wannan Gwamnatin dudu 4 da kwana 3 kan karagar mulki. Kenan in har laifin lalacewar makarantar za a nuna. To tabbas tsohowar Gwamnatinsu za a dorawa laifin domin a cikin shekaru takwas na mulkinsu ne makarantar ta lalace, kuma su ka ki gyarawa. Yanzu haka kasa da watanni biyu na wannan Gwamnatin ta bayar da kwangilar gyaran makarantannin Primary da dama a jahar Zamfara, Wanda dukkanin shuwagabannin Kananan hukumomin jahar Zamfara na jam'iyar PDP sun samu kwangilar. Karkashin hukumar UBE. Domin bunkasawa da farfado da Sha'anin ilimin da ya yi matukar tabarbarewa a jahar ta Zamfara. Haka zalika ko a watanni biyu da su ka shude mai girma gwamna ya ziyarci Makarantar, GDSS Sambo, da GDSS Birnin Ruwa. Da Unity Kwatarkwashi, Domin ganin halin da makarantun su ke ciki, Inda nuna bacin ransa na ganin halin da makarantannin su ke ciki, ya sha alwashin gyara su.
Abdulmalik Saidu Maibiredi.
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
October 2, 2019

