haka zalika yau lahadi 10-11-2019 sama da mutum dubu Hamsin su ka bar jam'iyar APC zuwa Jam'iyar PDP. Karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar Maradun Hon. Shehu Muhammad Faru. Daga cikin wadanda su ka canza shekar akwai shuwagabannin jam'iyar APC, na karamar hukumar, da tsofaffin 'yan majalissu na jahar Zamfara, kwamishinoni daga karamar hukumar ta Maradun. Da kuma tsofaffin masu baiwa gwamna shawara da Manyan mataimaka na musamman da Kuma wasu daga Kananan hukumomin Bukuyum Da Gummi Karkashin jagorancin Hon. Yusuf Zugu.
Da su ke bayyana dalillansu na canza shekar sun bayyana Cewa sun canza shekar ne saboda dalilan da su ka hada da Samar da tsaro da inganta tsaron da tallafawa ma'aikata ta hanyar biyansu hakkokinsu. da kuma tallafawa matasa da dalibbai.
Da ya ke jawabi Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara.
Ya bayyana godiyarsa GA Allah ta'allah da ya ke cigaba da ba shi nasara a cikin jagoransa. Haka Zalika ya yi godiya ga irin yadda Al'umma ke Goya masa baya. Ya kuma roki Al'umma da su cigaba da marawa gwamnatinsa baya da kuma addu'o'in da Al'ummar jahar ke cigaba da yi masa. Daga nan ya roki Al'ummar da su cigaba da addu'ar fatan alheri ga wannan gwamnatin.
Bikin karbar 'yan wankan ya samu halartar sanata Hassan Nasiha Gusau, Sanata Hassan Dan iya Anka, shuwagaban Jam'iyar PDP na jahar Zamfara. Alh. Ibrahim Mallaha Gusau, Hon. Jamilu Aliyu Zannan Gusau da Sauran jiga-jigan 'ya'yan jam'iyar PDP da Manyan makaraban gwamnatin jahar Zamfara.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
10th November, 2019

