GWAMNATIN ZAMFARA ZA TA DAWO DA MARTABAR KASUWANCIN JAHAR DA YA TABARBARE. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 12 November 2019

GWAMNATIN ZAMFARA ZA TA DAWO DA MARTABAR KASUWANCIN JAHAR DA YA TABARBARE.

Yau Talata 12-10-2019 Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon. Dr. Bello muhammad Matawallen Maradun ya karbi Bakuncin Cibiyar 'yan Kasuwa da masana'antu da aikin gona ta jahar Zamfara.

Da ya ke jawabi shugaban Kungiyar na jahar Zamfara Alh. Dr. Abdullahi  Maiwada Gusau (MON) Ya Fara da taya murna ga Mai Daraja gwamna tare da nuna goyon bayan Kungiyar dari-bisa ga Manuhohin gwamnan, musamman akan tarin nasarorin da gwamnatinsa ke samu musamman Akan sha'anin tsaro, tallafawa matasa da kuma mata da dawo da martabar jahar Zamfara a idon duniya. Haka zalika sun bayyana matukar farin cikinsu akan tarbo na ban girma da su ka samu daga gwamnan. Wanda su ka bayyana a matsayin muhimmin Abu da Kungiyar ba ta taba samu ba.

Daga nan shugaban ya bayyana damuwa akan yadda gudanar da baje-koli ya samu koma baya matuka gaya Wanda shekaru takwas baya an dena shirya baje-kolin Kirki a jahar Zamfara, Wanda ke tallafawa da bunkasa sha'anin cigaban kasuwanci. Tare neman gwamnatin jahar Zamfara ta gina masu ofis Wanda tun lokacin tsohuwar gwamnatin Mamuda aka roshe yayin yin Assibitin Yariman Bakura. Wanda zuwa yau 'ya'yan kungiyar ne ke  biyan kudin haya a duk shekara. Daga nan ya roki gwamnatin da ta tallafawa 'yan Kasuwa da bashi Marar ruwa, don cigaban kasuwancin jahar.

Da ya ke maida jawabi Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Matawallen Maradun, ya Bayyana godiyarsa Akan ziyara da su ka kawo masa tare da bayyana masu kyakkyawan tsarin da gwamnatinsa ta yi domin tallafawa 'yan Kasuwar jahar Zamfara tare da habbaka sha'anin noma domin cigaban jahar, inda ya bayyana matukar mamaki Akan yadda aka bar yin baje-koli a Zamfara duk da muhimmancinta ga cigaban tattalin arzikin jahar. Dan haka ya daukI alkawarin Mara masu baya Don tabbatar da sha'anin ksuwanci da noma ya habbaka. Inda ya alkawarta masu za a dawo da yin baje-koli a jahar Zamfara Wanda shi zai jagoranci shirya shi tare da tallafi Mai tsoka Don tabbatar da nasarar shirin. Haka zalika gwamnan ya yi alkawarin Gina masu ofis tare da baiwa 'yan Kasuwa bashi domin tallafawa kasuwancinsu.

Taron dai ya samu halartar Mai Daraja Mataimakin gwamnan jahar Zamfara Batista Mahdi Aliyu Gusau, Shugaban Jam'iyar PDP na jahar Zamfara, Alh. Ibrahim Mallaha Gusau, Shugaban ma'aikatan jahar Zamfara Alh. Kabir Balarabe, Tsohon Kakakin Majalissar Dokokin jahar Zamfara Rt. Hon. Bature Umaru Sambo. Da Sauran muhimman Jami'an gwamnati da 'yan Kasuwa da Manoma.

 Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
12th November, 2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here