A bangaren ma'aikatu yanzu An canza tsarin wasu ma'aikatu tare da hade wasu da kirkiro wasu wanda yanzu ma'aikatun za su kasance kamar haka:
1- Ma'aikatar Shari'a
2- Ma'aikatar Gona da albarkatun Kasa
3- Ma'aikatar Ciniki, Cigaban Kasuwanci da kuma yawon buda ido
4- Ma'aikatar Ilimi, Kimiya da Kere-kere
5- Ma'aikatar Muhalli, da Ginar albarkatun Kasa
6- Ma'aikatar Kudi
7- Ma'aikatar Kasafin Kudi da tsare-tsare-tsaren Tattalin arziki.
8- Ma'aikatar Raya Karkara da kungiyoyin cigaban kasa.
9- Ma'aikatar Tsaro da ayukkan Cikin gida
10- Ma'aikatar Lamurran Addini.
11- Ma'aikatar albarkatun Ruwa
12- Ma'aikatar Tallafawa Matasa da ayukkan hannu.
13- Ma'aikatar Watsa Labarai.
14- Ma'aikatar kananan hukumomi da Cigaban Al'umma.
15- Ma'aikatar ayukka da Sufuri
16- Ma'aikatar Lafiya
Ma'aikatar Mata da Kananan Yara da walwalar Jama'a.
Haka zalika gwamnan ya bayyana Cewa jahar Zamfara ita ce Jaha Mai mafi yawan Manyan Sakatarori har 47 wadanda tsohowar gwamnatin da ta shude ta Kai wasu daga cikinsu wannan matsayin ne, ba Don sun cancanta ba Don haka ga jarabawar da aka yi masu mutum 26 ne kurrum su ka ci jarabawar.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
14th November, 2019

