GWAMNA MATAWALLE YA CIKAWA ZAWUYYOYIN GUSAU ALKAWARIN DA YA DAUKAR MASU A LOKACIN YAKIN NEMAN ZABE. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Sunday, 17 November 2019

GWAMNA MATAWALLE YA CIKAWA ZAWUYYOYIN GUSAU ALKAWARIN DA YA DAUKAR MASU A LOKACIN YAKIN NEMAN ZABE.










Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya halarci ZAWUYYOYIN GUSAU wajen taron MAULIDIN FIYAYYEN HALITTU (S. A W).

Zawuyyoyin da gwamnan ya halarta cikin Daren yau sun hada da babbar zawuyyar Gusau, da karamar Zawuyya da zawuyyar Malam Aliyu Dango, Sai kuma zawuyyar shehu Salihu Na Malam Ango da zawuyyar unguwar Toka, Sai kuma zawuyyar Sheikh Malam Lawali Jibiya.

A lokacin ziyarar zawuyyoyin mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Ya yi godiya ga shehunnan zawuyyoyin akan irin Addu'o'in neman zaman lafiyar da su ke yiwa jahar Zamfara Wanda alhamdulillahi zuwa yanzu Zamfara ta samu zaman lafiya. Haka zalika ya yi godiya akan irin addu'o'in da zawuyyoyin su ke yiwa gwamnatinsa. Gwamnan ya bayyanawa Malamman Cewa kofar gwamnatinsa a bude take ga Malamman wajen Bayar da shawarwari  neman gudunmawarsu daga gwamnatinsa. Sai dai gwamnan ya bukaci Malaman da ba Sai sun shiga fadar gwamnatinsa wajen neman bukata ba, duk Abunda su ke nema su neme shi ya zo Ta hanyar makarabansa, ba Sai sun tako kafarsu a ofishinsa ba. A cewar gwamnan "Malamai Kun wuce ku zo gidan gwamnati Sai dai gwamnati ta zo gunku."

A jawabin malamman daban-daban sun yi godiya ga gwamnan Akan alkawarin da ya cika Masu lokacin yakin neman Zabensa, lokacin da ya zagaya zawuyyoyin Cewa ko ya zama gwamna zai rinka zuwa wajen mauludin ba wai yanzu dan yana son su Zabe shi ba. Haka zalika Malaman sun yiwa gwamnatinsa Addu'o'in samun nasara da zaman lafiya da samun yalwataccen arziki.

Ziyarar Mauludin dai ta samu halartar Tsohon Mataimakin gwamnan jahar Zamfara Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman, Shugaban jam'iyar PDP na jahar Zamfara Alh. Ibrahim Mallaha da Tsohon Kakakin Majalissar dokokin jahar Zamfara Rt. Hon. Bature Umaru Sambo, da Sauran muhimman Jama'a.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
17th November, 2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here