Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon (Dr) Bello Muhammad (Matawallen Maradun) ya yi kira ga dukkanin Al'ummar jahar Zamfara da su kwantar da hankalinsu, Ka da su ji ko dar akan wannan iftala'i da ya faru, su cigaba da baiwa gwamnatinsa hadin Kai da goyon baya, a kokarinsa na Samar Tsaron rayukka da dukiyoyin Al'ummar jahar baki daya.
Gwamnan ya nuna matukar damuwarsa akan aika-aika da 'yan bindiga suka yi a karamar hukumar mulkin Gummi. Ya kuma jajantawa dukannin iyalan wadanda su ka rasa rayukkansu da kuma wadanda su ka jikkata yayin wannan harin na 'yan bindigar.
Gwamnan ya kuma kara baiwa Al'ummar jahar Zamfara tabbacin Cewa gwamnatinsa Tana akan bakanta na sasanci da wadanda su yarda su ka mika wuya, Dan haka gwamnatinsa ba za ta zura ido ga wasu daidaiku da ba su son a zauna lafiya su bata cigaban da aka samu na zaman lafiya a jahar ba, a cewarsa
"Tun daga Fulani da Yan-sa-kai duk sun fahinci shirinmu na sasanci domin Samar da zaman lafiya kuma suna biyayya ga gwamnatin. Sai dai wasu tsiraru da ba su son a zauna lafiya su ke ta shige da fice Don ganin wannan shirin ya samu nakasu, don haka su ke son su watse shi, saboda nufinsu na ganin Zamfara ba ta zauna lafiya ba, Saboda wata buyayyar manufa tasu,"a cewar gwamnan.
Daga nan gwamnan ya baiwa Al'ummar jahar Zamfara tabbacin Cewa gwamnatinsa ba za ta zura ido makiya su kassara jahar ba. Don haka a Madadin shi kansa, da dukkanin makarabansa da duk masu yiwa Al'ummar jahar Zamfara fatan zaman lafiya. Suna Mika sakon ta'aziya ga 'yan uwan wadanda ka rasa rayukkansu Allah ya jikansu da rahama ya sa sun huta Ya sa aljanna firdausi ce a makomarsu, su kuma wadanda su ka jikkata Allah ya ba su lafiya.
Zailani Bappa
SSA Media.
Fassara
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
19th November, 2019

