GWAMNATIN ZAMFARA TALLAFAWA IYALAN WAƊANDA SU KA RASA RAYUKKANSU TARE DA ƊAUKAR NAUYIN ƊAWAINIYAR JINYAR WAƊANDA NA JIKKATA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 19 November 2019

GWAMNATIN ZAMFARA TALLAFAWA IYALAN WAƊANDA SU KA RASA RAYUKKANSU TARE DA ƊAUKAR NAUYIN ƊAWAINIYAR JINYAR WAƊANDA NA JIKKATA.




Gwamnatin jahar Zamfara ƙarƙashin jagorancin hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ta ziyarci ƙaramar hukumar mulkin Gummi, domin ganewa idanunta aika-aikar da 'yan bindiga su ka yi a ƙaramar hukumar. Tare da Miƙa sakon ta'aziyarta ga iyalan waɗanda su ka rasa rayukkansu, da kuma jajantawa ga waɗanda su Ka jikkata da kuma hasarar dukiyoyi.

Tawagar wadda mai Daraja Mataimakin gwamnan jahar Zamfara Hon. Barista Mahdi Aliyu Gusua, ke jagoranta. Ta miƙa ta'aziyarta ga iyalan waɗanda su ka rasa rayukkansu tare da jajantawa waɗanda su ka jikkata da hasarar dukiyoyinsu.

Gwamnan ya shiga babbar assibitin Gummi domin ganin waɗanda suka jikkata tare da miƙa tallafin gwamnatin jahar Zamfara na Naira dubu Hamsin ga duk wanda ya samu rauni tare da ɗaukar nauyin jinyarsu, har su warke. Haka zalika gwamnatin za ta baiwa dukkanin iyalan waɗanda su ka rasa rayukkansu naira dubu ɗari biyu da Hamsin da kuma buhun shinkafa biyu.

Da ya ke jawabi Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Wanda Mataimakin nasa ya wakilta, ya nuna matuƙar kaɗuwarsa ga wannan ifatala'i, inda ya yi alƙawarin gwamnatinsa  ba za ta taɓa bari, waɗanda ba su gurin Zamfara ta zauna lafiya, su runtsa ba. Inda ya bayyana Wanda su ka yi wannan aikin a matsayin Manyan maƙiya jahar Zamfara, tare da Bayar da tabbacin Cewa insha Allahu Sai Zamfara ta zauna lafiya ko da wasu ba su so.

Daga ƙarshe ya roƙi Allah subhanahu wata'ala ya jiƙan waɗanda su ka rasa rayukkansu, su ku waɗanda su ka jikkata ya roƙi Allah ya ba su lafiya, tare da maye masu gurbin dukiyar da su ka rasa.

Da ya ke jawabi Mai martaba Sarkin Mafaran Gummi mai Shari'a Alh. Lawal Hassan Gummi. Ya nuna matuƙar jin daɗinsa da wannan ziyarar da gwamnatin ta kawo masu, ya kuma yi alƙawarin Cewa masarautar Gummi za ta Bayar  Da goyon bayanta da ɗari-bisa-ɗari Don ganin an murƙushe bata garin da ba su son a zauna lafiya.

Daga cikin Waɗanda su ka halarci wannan Ta'aziya akwai sakataren gwamnatin jahar Zamfara Hon. Bala Bello Maru, Ɗan Majalissar tarayya mai wakiltar Gummi da Bukuyyum Hon. Engr. Suleman Abubakar Gummi Da takwaransa na Gusau da Tsafe, Hon. Kabiru Amadu Maipalace. Sai kuma Mai baiwa gwamna shawara Akan sha'anin tsaro Hon Abubakar Dauran Justice Da Sauran jiga-jigan 'yan siyasa.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
19th November, 2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here