Tun shekaranjiya su ke yada labarai a kafar Sada zumunta ta zamani Social Media Cewa, mai Daraja gwamnan jahar Zamfara. Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya wanke kafarsa ya yi kasar Germany duk da kashe-kashen da aka yi a karamar hukumar mulkin Gummi. Cewa bai damu da kisan rayukka da dukiyoyin Al'ummar jahar ba.
Sai dai Abunda a ba su sani ba akwai matukar rata tsakanin gwamna Matawalle da Wanda su ke biya Wato Tsohon gwamna Abdulazizu Abubakar yari. Wanda DUK kashe-kashen gillar da aka yi a jahar Zamfara a lokacin mulkinsa. Hakan bai sa ya dena yawace-yawacen banzar da ya ta yi ba.
Alhamdulillahi yanzu Allah ya baiwa jahar Zamfara, gwamna mai kaunar Al'ummarsa, Wanda tun da ya hau kan karagar mulki, kullum gurinsa shi ne Al'ummar jahar Zamfara su zauna lafiya. Su yi barci da ido Biyu. Idan ba mu manta ba tun daga ranar da mai daraja gwamna ya karbi jagorancin jahar Zamfara. Ya yi alkawarin duk ya bar jahar to zai tafi neman ayukkan da za su Ciyar da Zamfarar gaba ne, haka zalika gwamnan ya yi alkawarin ba zai tafi yawon kawai ba, da dukiyar talakawan jahar Zamfara ba.
Wanda alhamdulillahi kasar Germany Ta turowa mai Daraja gwamnan jahar takardar gayyata Inda zai gabatar da mukala tare tattaunawa akan bunkasar jahar Zamfara. Ta hanyar ilimi da kuma dogaro ga Kai, Wanda su ka shirya yi a yau, 20-11-2019. Sai dai ganin halin da Al'ummar garin Karaye su ke ciki ya sa Mai girma gwamna ya soke wannan tafiyar duk da alfanunta ga Al'ummar jahar Zamfara domin bai Kai rayukkan Al'ummarsa.
Wanda alhamdulillahi Mai girma gwamna ya tsaya domin binciken yadda aka haihu a ragaya tare da daukar matakan da su ka dace domin ganin hakan bai ta sake aukuwa ba.
Kwatsam Sai ga wannan labarin, ya fito daga magoya Tsohon gwamnan jahar Zamfara Abdulazizu Abubakar yari Cewa Gwamna ya wuce Germany.
Alhamdulillahi mu duk inda Gwamna Matawalle Zai tafi yakan sanar da Al'ummarsa Abunda zai tafi yi, haka in ya je yakan fadawa duniya Abunda ya Kai shi ta hanyar bidiyo da hotona dama jawabai daga masu taimaka masa a bangaren watsa labarai, ba kamar ku da lokacin mulkinku ku ke yin komi a Rufe ba.
Yanzu haka mai girma gwamna yana cikin jahar Zamfara a fadarsa. Kamar yadda ku ka gani a hoto ga shi tare da mai Martaba Sarkin Maradun Alh. Garba Tambari.
Don haka ina ganin wannan rubutun naku tamkar dabawa kanku wuka ne kuka yi, kuka koma gefe kuna Kirari. Domin halayen mai gidanku ne, ku ka bayyana duniya. Kuma Al'ummar jahar Zamfara ba Mahaukata ba ne.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
20th November, 2019








