GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA TA KADDAMAR DA SHIRIN TURA 'YA'YAN TALAKAWA 200 KASASHEN WAJE KARATU. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Sunday, 1 December 2019

GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA TA KADDAMAR DA SHIRIN TURA 'YA'YAN TALAKAWA 200 KASASHEN WAJE KARATU.


Tun Bayan da gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun ya karbi jagorancin jahar Zamfara, ya dauki aniyar dawo da martabar ilimin jahar Zamfara,da ya tabarbare, ta hanyar tallafawa Kowane bangare na ilimin jahar ta yadda za a samu Al'umma masu ilimin taimakawa  jahar.

Hakan ne ya sa gwamnan ya dauki aniyar tura ya'yan talakawa 200 daga jahar Zamfara zuwa kasashen wajen domin karatun ilimi fannoni da Dama na ilimin kimiya da fasaha da mu ke da matukar karancinsu a jahar Zamfara.

Wadannan dalibbai dai an zakulo su ne, ta hanyar shirya masu jarabawa, inda aka tace-tace mutum 200 daga kananan hukumomin jahar Zamfara 14. Dalibbai dai za su tafi kasashen China, Cyrus, India da Sudan. Haka zalika mafi yawa daga cikin wadanda su ka samu wannan damar 'yan talakawa ne, wasu ma marayu ne daga gidan Marayu 

Da ya ke jawabi Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, Wanda Sakataren gwamnatin jahar. Hon. Bala Bello Maru. Ya Waklita.

Ya bayyana Cewa gwamnatin jahar Zamfara ta yi wannan yunkurin ne, domin tabbatar da Cewa an tallafi 'ya'yan talakawan Zamfara. Gwamnan ya bayyana Cewa cancantarsu ce ta sa aka zabo su, Dan Haka ya yi kira gare su da su zama jakadu nagari ga jahar da kuma yin Karatu Don taimakawa Al'ummar jahar Zamfara din.

Da ya ke jawabi daya daga cikin wadanda su ka amfana da wannan shirin wanda yana daga cikin marayu. Ya bayyana matukar jin dadinsa da wannan shirin da gwamnan ya bullo da shi, tare da bayyana Cewa, insha Allahu, ba za su ba maradda kunya ba. 

Bikin kaddamar da ya samu halartar wannan bikin, ÆŠan Majalissar Dattawa mai wakiltar Zamfara Ta Tsakkiya Hon. Hassan Muhammad Nasiha. Shugaban Jam'iyar PDP Wanda Hon faruk  Shattiman Rijiya ya Waklita Hon. Yusuf Alhassan Kanoma, Sai kuma Mai baiwa gwamna shawara Akan sha'anin Dalibbai Hon. Lukman Majidadi Da Sauran jiga-jigan 'yan siyasa. Iyayen Dalibbai da shuwagabannin kungiyar Dalibbai ta Jahar Zamfara (NUZAMSS)
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
1st  December, 2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here