DALIBBAI 50 DA GWAMNATIN ZAMFARA TA DAUKI NAUYIN KARATUNSU, SUN BAR NIJERIYA ZUWA KASAR SUDAN. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 3 December 2019

DALIBBAI 50 DA GWAMNATIN ZAMFARA TA DAUKI NAUYIN KARATUNSU, SUN BAR NIJERIYA ZUWA KASAR SUDAN.

Dalibban dai da su ka hada da 'ya'yan talakawa da Marayu gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ta dauki nauyin su ne, domin su karancin ilimin Likitanci da Aikin Jinya (Medicine and Nursing). Domin cike gibin da jahar ta ke da shi na karancin wadannan fannoni.

Dalibban da su ka hada da mata 22 maza 28, mata 10 za su Karanci Medicine yayinda 12 za su yi Nursing. Maza 18 ne za su karanci Medicine yayinda 10 za su karci Nursing

Dalibban sun tashi da Misalin karfe 10:30 na safe a Filin jirgin saman kasa-da-kasa na Malam Aminu International Airport  Kano, da ke Kano. Cikin Kamfanin Badar Airline.

Wannan shi ne kashin farko na dalibbai 200 da gwamnatin jahar ta dauki nauyin karatunsu. Sauran 150  za su tafi kasashen China, Cyprus da India.

Tawagar dalibban dai na karkashin jagorancin Hon Lukman Majidadi, Consultant Muhammad Jazuli Musa, da Director Of Finance Zamfara state Scholarship Board Alh. Garba Haruna Ma'aji.

Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
3nd December, 2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here