GWAMNATIN ZAMFARA. TA RANTSAR DA KWAMISHONI 19 DA MANYAN MASU BATA SHAWARA. 30 - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 5 December 2019

GWAMNATIN ZAMFARA. TA RANTSAR DA KWAMISHONI 19 DA MANYAN MASU BATA SHAWARA. 30





Gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Gwamnan jahar Hon Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun. Ta rantsar kwamishonin jahar da Manyan masu bata shawara.
Mutanen da aka rantsar sun hada da shugaban ma'aikatan jahar Zamfara Alh Kabiru Balarabe (Sardaunan Dan-isah) da Kwamishinoni 19 tare da Manyan masu baiwa gwamna shawara na musamman su 30. Da kuma babban Sakatare na dindin.
Bikin rantsuwar da ya gudana ne a fadar gwamnatin jahar da ke Gusau. Wadda mai babbar mai Shari'a ta jahar Kulu Aliyu, ta yi.
Da ya ke jawabi Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara, ya taya wadanda aka rantsar Murnar samun wannan matsayin tare da shawartarsu da su yi aiki tukuru domin cigaban jahar Zamfara, tare da zama masu amfani ga Al'ummar jahar. Haka zalika gwamnan ya yi kira ga Al'ummar jahar su tabbatar sun baiwa wadannan bayin Allah gudunmawa domin samun nasarar aikin su.
Bikin  Ya samu halartar Mai Daraja Mataimakin gwamnan jahar Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau, Sakataren gwamnatin jahar Zamfara Hon. Bala Bello Maru, Shugaban ma'aikata a Fadar gwamnatin jahar Zamfara Alh. Bala Mande , Shugaban Majalissar Sarkunan jahar Zamfara Sarkin Anka mai Martaba Alh. Ahmad Muhammad Attahiru, shuwagabannin Kananan hukumomin jahar Zamfara  Da Sauran muhimman Jami'an gwamnati da masu yiwa wadannan aka rantsar fatan alheri.
*Abdulmalik Saidu Maibiredi*
Senior Special Assistant to the Governor Of Zamfara State
5th December, 2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here