KUNGIYAR AdvocacyNigeria TA YI GAGARUMIN TARON WAYAR DA KAI TARE DA MATA 'YAN SIYASA A ZAMFARA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 11 December 2019

KUNGIYAR AdvocacyNigeria TA YI GAGARUMIN TARON WAYAR DA KAI TARE DA MATA 'YAN SIYASA A ZAMFARA.

Kungiyar AdvocacyNigeria kungiya ce da ta kwashe sama da shekaru shida Tana aiki a jahar Zamfara. Inda take fafutuka wajen yaki da mutuwar mata wajen haihuwa da kuma yara kanana da kuma cin hanci da rashawa a assibitocinmu. Tare da fadakar da Al'umma akan sanya ido domin yakar cin hanci da rashawa.

Taron Wanda ya gudana a dakin taro na hukumar Zakka da ke Bye Pass Gusau.

A wurin taron Dr. Mannir Bature Daga assibitin Tarayya Gusau, ya bayyana irin matsayi da yanayin mutuwar mata da kananan Yara ya ke ciki a jahar Zamfara, tare da wayarwa matan kai akan hanyoyin da ya kamata matan su bi domin inganta sha'anin kiyon lafiyarsu, tare da tabbatar da gwamnatoci sun aiwatar da kasafin kudin da su ka yi a bangaren kiyon lafiya.

Daga nan aka shiga tattaunawa tsakanin jami'an kiyon lafiya, da uwayenmu mata 'Yan siyasa. Domin ganin an samu sauyi matuka gaya a wannan bangaren domin samun sauyi don ceto mata masu juna, da yara kanana. Inda kowane bangaren ya fadi yanayin da ya ke ciki da kuma gudumawar da ya ke iya bayarwa wajen magance wadannan matsalolin.

Taron dai ya gudana ne karkashin jagorancin Alh. Abdulahi Lere mukaddashin shugabar AdvocacyNigeria tare da shugaban wannan kungiyar a jahar Zamfara. Alh. Rabiu Sambo da sauran mata 'Yan siyasa da 'Yan Gwaggwarmaya.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here